Aikin Hajji, Ire-iren Aikin Hajji da Kuma Falalarsa

Aikin Hajji

Kafin na ce komai game da aikin hajji wanda na daya daga cikin manyan rukanai biyar da aka gina addinin musulunci akai zan so mai karatu ya yi sani cewa; mawallafin nan (ni) ba malami ba ne, kuma komai na wallafa na yi shi ne bayan dogon bincike da na gabatar game da wannan rukuni na hajji.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

‘Yan‘uwa musulmi, malamai, almajirai da sauran ya ayyuhannasi, in har kun ga wani kure da na kuskure a cikin rubutun nan ku yi hanzarin sanar da ni ta adireshin email dina; info@seeyblog.com.ng domin a yi gyara.

Allah ya saka muku da alkhairi ameen.

Duk wani cikakken musulmi ba ya bukatar a gabatar masa da menene aikin hajji muddin ba sabon shiga musulunci ba ne.

To, amma sakamakon muna son yin jawabi dalla-dalla a kan abinda muke son gabatar muku za mu fara da yin warwara a kan menene shi kansa aikin hajji.

Menene Aikin Hajji

Daga cikin rukunai biyar da aka gina addinin musulunci akai akwai:

  1. Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu (S.A.W.) mazonsa ne
  2. Tsai da Sallah
  3. Ba da Zakkah
  4. Yin Azumin Watan Ramadan 
  5. Da Aikin Hajji (ga duk wanda Allah ya horewa kuma ya bashi iko)

Hakan na nuni da cewa, aikin hajji ya wajabta akan kowanne musulmi amma fa idan yana da hali da ikon yinsa.

Dan’uwa musulmi in har ka samu damar yin aikin hajji (Wato Allah ya hore ma) to zan so kwadaitar da kai zuwa aikin hajji domin shi da zarar Allah ya hore maka, to niyya kawai ta rage maka.

Madallah.

“Aikin Hajji daya daga cikin nau’ikan ayyuka ne da ake yi a addinin musulunci wanda musulmin duk duniya ke zuwa kasar Makkah (Bakka), Saudi Arebiya don su aiwatar da wadansu ibadoji.

“Su wadannan ibadoji sun hadar da hawa arfa, yin safa da marwa, zagaya dakin Ka’abah (Dawafi), ziyarar Ma’aiki (S.A.W.), jifan shaidan (la’ananne) da sauransu.

Allah Madaukakin Sarki ya fada a suratul Al’Imrana, aya ta 97 inda ya ce, “Kuma akwai hakkin dakin domin Allah a kan mutane, ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta, to, lalle Allah Mawadaci ne daga barin talikai.”

Kuma a cikin suratul Bakara, aya ta 196 ya ce, “Kuma ku cika aikin hajji da umra domin Allah.”

Lallai ko in haka ne, Allah ya umarci dukkanin musulmi da su cika aikin hajji in har suna da dama da ikon yinsa, saboda haka ya kamata duk wanda Allah ya hore masa abin zuwa kada ya bari a bashi labari.

Ire-iren Aikin Hajji

Aikin Hajji ya karkasu har zuwa rabe-rabe ko ire-ire guda uku:

  1. Ifradi: shi hajj ifradi shi ne aikin hajjin da alhaji zai dauki niyyar yin aikin hajji ne kurum ban da umara.
  2. Tammatu’i: shi ko haji tammatu’I shi ne hajjin da alhajji zai yi niyyar umara a cikin watannin aikin hajji, kuma ya fita daga wato ainihin cikin ihraminsa, sa’annan sai kuma ya yi niyyar yin aikin hajji a cikin wannan shekara da ya gudanar da umararsa.
  3. Kirani: shi ne hajjin da alhaji zai yi niyyar yin hajji da umara a tare.

Falalar Aikin Hajji Da Umara

Hajji da umra suna daga cikin ayyuka mafi falala wadanda suke kankare zunubai da kurakurai, kuma masu kusantarwa zuwa yardar Allah Madaukaki da aljannarsa.

Domin kuwa duk wanda yayi hajji kuma bai yi jima’i ba da fasikanci, zai koma kamar ranar da uwarsa ta haifesa (na rashin zunubai).

Haka kuma hajjin da yake kararre bai da sakamako face Aljannah.

Lalle ne an tambayi Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) game da aiki wanda ya fi duka (aiyuka) falala, sai yace: (Imani da Allah da Manzonsa), sai kuma akace (Sai kuma me?) yace: (sai kuma Jihadi cikin hanyar Allah) sai kuma akace: (Sai kuma me?), sai yace: (Sai hajji kararre) – Buhari da Muslim ne suka ruwaitoshi.

Kuma Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbatar a gare shi) yace: (Umra zuwa wata umra, tana kankare zunuban da ke tsakaninsu, kuma hajji wanda yake kararre bai da sakamako face Aljannah) – Muslim ne ya ruwaito shi.

Haka kuma Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbatar a gare shi) yace: (Wata Umra ce cikin Ramadan tana daidai da yin hajji tare da ni) – Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Bisa la’akari da hujjojin da ke sama ta fuskar hadisan Annabi, za mu ga cewa, lallai falalar da aikin Hajji da Umra ke da ita ba ‘yar karama ba ce.

Madogararmu: littafin Hausa Description of Hajj and Umrah with selected duas da kuma shafukan yanar gizo sahihai da muka gudanar da binciken tsaf ta cikinku.

Kammalawa

Za mu daure tabarmar nan sai kuma kun sake jinmu a rubutu na gaba wanda za mu kawo muku ainihin kudin aikin hajji na wannan shekarar da muke ciki.

Muna son kara fadada bincike ne daga sassa daban-dabam domin nemo muku ingantattun bayanan da za su amfaneku.

SeeDesk.

Previous News Next News