A iya nawa wawan tunanin babu wata irin nasara da ake cimma wa ta sauki ba tare da wata sadaukarwa ba.
Kuma ita tulin tsoka ana iya tara ta cikin sauki da salama har ta zama teba kai har ta hado da ‘dan marayan ciki ko dirkeken tumbi.
Amma fa yayin da aka waiwaici wannan tararriyar tsoka, kuma ake son lallai sai an zazzageta ta dawo daidai wadaida, to, ko tantama a cire sai an yi gumi, an yi haki, an ci uwa da uba kafin a samu a rage tsokar nan.
Ko-da-ya-ke na ji labarai iri-iri game da masu maganin gargajiyar da ke bayar da magani a sha tumbi ya sauka, kuma kiba ma ta ragu, tebar jiki ita kanta ta sauka cikin sauki.
Amma dai gogan naku bai taba gwadawa ba, kuma ni na ma fi ganewa motsa jiki duk da wasu daga cikin magungunan da ake bayarwa suna aiki.
Bakona, ina maka lale marhaban da zuwa shafin nan mai albarka na SeeyBlog wanda gamayyar editocin SeeyDesk ke gudanarwa.
Yau, da yarda Allah zan yi bayani ne game da tumbi, kiba da kuma teba, sa’annan na kawo muku nau’i-nau’in magungunan rage su na gargajiya har ma da na baturen in akwai shi.
A karshe kuma na baku shawarar da ta dace a kan ina mafita kuma me ya fi kamata ku yi.
Menene Tumbi
Tumbi (belly) kayan adon Alhazan Arewa, masu kudi da ma wadanda ke tunanin su hutattu ne kai har ma da ayyuhannasic (wato ya ku bayi irinmu).
Yawan zama a wuri daya ba tare da yawo ko gudu ba na iya haifar da tumbi, haka kuma ci a kwanta ma na iya haifar da kibar jiki da tumbi.
Don haka in dai burinka da muradinka shi ne; ka ga ka rage wannan uwar rindimemen cikin naka kamar na mai ciki to maza ka shirya domin lallai sai ka yi da gaske.
Yadda Ake Rage Tumbi
Hanya mafi al’ala ta rage tumbi ita ce; ta hanyar fita jogging, gudun safiya da kuma yawan yin activities wanda jiki zai san ana motsa shi.
Sannan sai kula da abincin da mutum ke ci, ku rage yawan cin abinci mai high carbon a ciki.
In da son samu ne ma ku yi kawance da cin kayan marmari, gudun motsa jiki da kuma abincin ganye domin rage ba iya tumbinku ba, kai har ma da sauran jikinku ya dawo fitted.
Ku yi sani cewa; babu wani da ake cimma wa nasara a kansa ba tare da commitment ba, da kuma juriya.
Kada ku yi saurin mika wuya saboda kun sha wuya yau, gobe, ko jibi. Ku yi yaki da zuciyoyinku ku yi ta yi har ku kai ga nasara.
Maganin Rage Tumbi
Babu wata cuta da Allah ya saukar ba tare da maganinta ba, sai dai in maganin ne ya yi wuya, amma muddin ana nemansa to za a iya samu watan watarana.
Gwargwadon girman tumbinka ko girman tumbinki haɗe da girman hips to kuwa gwargwadon kusancinka da ciwon zuciya.
Ma'ana qarin girman tumbi ko hips daidai ya ke da qarin hatsarin gamuwa da bugun zuciya.
Haka ma haɗuwa da Hawan jini da ciwon sugar duk.
Tumbi abu ne mai sauƙin tarawa saide kwai wahalar narkarwa, sai mutum yayi da gaske.
Maganin Rage Tumbi na Daya
Da fari ku samo;
- Lemon tsami
- Citta danye
- Tafarnuwa (in kuna so, amma ba wajibi ba ce)
- Sai Zuma
Yadda Ake Hada Shi
Ku goga ko markada lemon tsaminku da cittarku da tafarkuwarku, bayan kun gama sai ku juye a cikin tukunya, sa’annan ku zuba ruwa kofi daya a ciki ku tafasa su.
Bayan kun tafasa sai ku sauke, ku barshi ya yi sanyi, ku tace sa’annan ku kawo zumarku a ciki ku gauraya sosai.
A karshe, ku rinka sha kafin ku kwanta barci.
Ku yi haka har tsawon kwana 7 ko sati biyu, da yardar Allah za ku ga canji ya samu.
A kula: mace mai ciki ko mai shayarwa kada ta yi hadin nan, sai dai ta tasafa ganyen tsamiya, ta tace shi, idan ya yi sanyi ta sa zuma a ciki ta sha.
Kamar yadda mawallafansa su ka bayyana, sun ce yana maganin infection, kuma mai fama da rikicewar al’ada ma zai iya bata matsala in ta sha wannan hadin.
Ko ma dai menene, Allah shi ne mafi sani.
Maganin Rage Tumbi na Biyu
Bayan tsananta binciken da muka yi, mun kara samo wani maganin rage tumbin, saboda haka sai ku gwada shi ku gani ko Allah zai sa a dace cikin sauki ba tare da an wahala ba.
A samo;
- Ruwa
- Na’a-na’a
- Lemon tsami
- Ginger (Danyar Citta)
- Da cucumber
Yadda Ake Hada Shi
Ku samu ganyen na’a-na’a danye guda 12, sai danyar dakakkiya ko markadaddiyar citta cikin dan karamin cokalin shan shayi 1, da cucumber madaidaiciya guda 1, da lemon tsami guda 1.
Sai a samu mazubi a hadesu wuri guda, a sa ruwa lita 1 a tafasa su amma kada fa a bari tiririnsu ya fito waje, bayan ya tafasa sai a sauke shi.
Sai a tace a rinka sha sau biyu a rara tsawon sati biyu. Da yardar Allah cikin kwanaki uku kacal za a ga canji.
A shawarce: ku daina kwanciya bayan kun ci abinci, ku rinka dan zazzagayawa domin ba wa jikinku damar nika abincin ya tura shi wuraren da suka dace da shi.
Mecece Kiba
Kamar yadda na bayyana a cikin rubutun da ya gabata, “maganin karin kiba na bature da na gargajiya” na ce, “Kiba na nufin karuwar nama a jiki sakamakon rashin motsa jiki, ko kumburashi ta hanyar magunguna da allurori, ko kuma ta dalilin yawan motsa jiki ko daga karfe kullum.”
To, in ko haka ne lallai kiba na samuwa ta hanyoyi mabambanta,akwai ta Allah da Annabi akwai kuma ta Allaro.
Sai dai, kiba dalilin yawan motsa jiki ba kasafai ta ke zama ciwo ba muddin an bi hanyoyin da suka dace wurin yinta. Kai kwarjini ma take kara wa mutum.
Yanzu, sai mu tsallaka kan maganin rage kiba
Maganin Rage Kiba
Na fada kuma gashi zan kara, babu wani sahihin maganin rage kiba fiye da motsa jiki da kuma daidaita abincin da ake ci, ko-da-ya-ke, wasu masana binciken lafiya a shekarar 2011 sun gano wani magani wanda nan gaba kadan za mu kawo muku sunansa.
Za mu fara da kawo maganin rage kiba na asibi, sai kuma na gargajiya, sai kuma mu kammala da hanyar rage kiba ta hanyar motsa jiki da daidaita cima.
Maganin Rage Kiba na Asibiti
In dai kana son ka rage kiba ta hanyar shan maganin asibiti, to, ka kwantar da hankalinka domin kakarka ta yanke saka.
Akwai wani maganin asibiti mai suna, “Adipotide” sahihi ne wurin taimaka wa mutane masu kiba su rage ta.
In da son samu ne, ku yi magana da likita wanda ku ke kusa da shi domin ya baku shawara game da maganin nan na adipotide, da kuma ka’idojin shansa, da kuma illolinsa.
Bayan shi, babu wani maganin rage kiba na asibiti wanda bincikenmu ya bamu. Ina dada gargadarku da kada ku sha maganin nan har sai kun tuntubi shawarar masana.
Hanyar Rage Kiba ta Zahiri
Babu wata zahirtacciyar hanyar da mutum walau mace ko namiji zai bi wajen rage kibar da ke damunsa fiye da;
- Ku rage ciye-ciyen kayan maiko masu carbon da yawa
- Ku yawaita shan ruwa akai-akai da zirga-zirga
- Ku rinka motsa jiki, walau hawan igiya, gudun safiya ko wani abu makamancin haka
- Ku yawaita cin abincin ganye irin su salad da sauransu
- Ku rinka cin kayan marmari irin su kankana, lemo, ayaba, abarba, gwanda da sauransu.
A karshe kuma ku daidaita lokacin cin abincinku, misali in kai sau uku za ka na cin abinci kullum to ana son ka daidaita lokutan cin abincin, sannan ka rinka dan yin dogon tattaki bayan ka ci abincin.
Overall dai, motsa jiki da daidaita abinci su ne hanya mafi nagarta wurin rage kiba cikin sauki.
Mecece Teba
Hajjaju teba na nufin taruwar nama a inda ba matsuguninsa ba, misali bayan wuya, kasan haba, kumatu, gefen ciki, cinyoyi har ma da fuska.
Kuma ita lalatar teba daya ce; wato naman wani guru-guru ya ke yi, in ka zauna, ko kana tafe.
Kazalika ana samun teba ta hanyoyi fitattu kuma sanannu, wato ci ba bisa ka’ida ba, da kuma yawan lalaci da rashin motsa jiki.
Duk dadin da jikinka zai ji muddin ba ka motsa shi to kana zaune za ka ga teba ta fara yi maka sallama a wasu sassa na jikinka.
Maganin Rage Teba
Alhaji da Hajiyar Allah wallahi tallahi babu wata hanyar rage teba da ta wuce ku motsa jiki, ku yawaita shan ruwa da kuma cin kaya ganye da sauran proteins.
Kada wani ya yaudareku ya baku wasu dure-dure ku je ku yi ta diddika kuma bukata ba ta biya ba.
Abu na farko da za ku yi shi ne; ku fara da yawan shan ruwa fiye da yadda kuka saba.
Sai kuma ku fara yi wa su shinkafa, taliya cin baya-baya.
Ku kuma rike wa su nono zallarsa, abincin ganye irin su salad wuta yadda ya kamata.
Sannan ku rinka motsa jiki na mintuna 60 kullum. Sai dai lokacin da za ku fara, ku fara da minti biyar, zuwa goma, zuwa sha biyar har ku je mintuna 60 din nan.
Ku kuma rinka rage yawan zama da yawan barci.
Allah shi ne masani.