Mecece Shagwaba da Yadda Ake Shagwaba Ga Saurayi ko Maigida

Shagwaba

Lokacin da na yi arba da wannan tambayar na yawon terere a yanar gizo sai da na tuntsure da dariya, ba fa dariyar keta ba, a’a, dariyar mamaki.

Sakamkon tambayar na ji ta har cikin raina ta min wani bambarakwai.

Eh mana, yo duk macen da ba ta iya shagwaba ba ai ina tunanin marabarta da garkeken gansamemen gardi kamata ‘yar kadan ce.

To, kamar dai yadda aka saba, zan fara da yi muku barka da zuwa shafin nan namu na SeeyBog mai albarka da kuma tarkace iri-iri.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Kuma yau Daktan naku zai yi muku fahimtacce kuma cikakken bayani a kan yadda mace za ta yi wa mijinta, saurayinta ko maigidanta shagwaba har ya ji cewa shi fa duk duniyar nan ta maliki yaumiddinin babu wata mace wacce ya ke marmari da muradin haduwa su zauna inuwa daya da ita facce ke.

To amma kafin haka bari na fara da baku labarin wata kawata ‘yar ajinmu shagwababbiya, wacce yanzu haka ba ma tare, amma fa na matukar yin crushing a kanta. Kawai ba na son alakarmu ta baci ne, shi yasa ban bayyana mata ina sonta ba.

Yarinyar sunanta Bilkisu, kuma tare muka fara Diploma da ita, hakika ni dai tunda nake ban taba haduwa da diya macen da na ji ta kwantamin a raina ba fiye da ita.

Saboda tsabar shagwabarta kusan kowa a cikin class dinmu ya santa, Bilkisu shagwaba, in ta bukaci ka bata aron littafi ka hana ta, sa ta kwantar da murya cikin irin salon kissar nan ta ce, “Kai ko saurayina yanzu ni ce ba zaka bai wa littafin ba?”

Ina muku rantsuwa da Allah da wuya ba ta san yadda ta shagwabance maka ka bata littafin nan ba, ga ta doguwa kyakkyawa, abin kam sai son barka.

Ni da yake mun saba da ita, kusan kowa a ajin nan namu yana referring dina da saurayinta ne, alhali kuma kawai kawance muke da ita.

Eh to in nace muku ba na sonta, to na yi muku karya, ko tafiya ce ta kama mu a jere muke tafe muna zantawa.

Amma dai kam, da za ki iya ko da kaso 80 din shagwabar Bilkisu ne, ina gaya miki da saurayinki ko megidanki ya mai dake yar gaban goshi, wato yar lelensa.

Shi yasa tun bayan rabuwarmu da ita, na kasa yin budurwa, kuma in dai ba wani kadaru na Allah ba ina fatan sake haduwa da ita mu zauna wuri daya kuma inuwa daya.

Bani son cikaku da surutun tsiya, amma bari mu shiga abinda ya tara mu a nan kai tsaye.

Mecece Shagwaba

Shagwaba dai wata irin dabi’ace wacce in da son samu ne ake da bukatar mace ta iya sosai. Ana son mace ta iya nau’ikan shagwaba iri-iri, kamar su shagwabar murya, fuska, motsin jiki da sauransu.

Ita fa shagwabar nan na taimakawa sosai wurin janyo hankalin namiji ya miki abinda kike so, amma fa zai fi kyau ki kula ki san wanne lokaci ya kamata ki na yi wa mijinki shagwaba.

Mafiya lokutan da mazaje ko samari ke son shagwaba to lokacin da suke cikin nishadi ne, amma in har kika yi masa shagwaba yayin da yake cikin wata damuwa abin bata masa rai zai kara yi.

Misali, mijinki na tsaka da hutawa, ki zo ki kwanto kansa kirjinki a kan nasa fuskarki dauke da murmushi. 

Ko kuma in za ki rokeshi wani abu ki yi irin yar marairaicewar nan kina kissar shagwaba kamar za ki yi kuka (amma fa ba kuka ba ne) ki ce, “haba baby ya kamata ka yi min ankon nan please”

In kuma budurwa ce, duk lokacin da za ki tambayi saurayinki wani abu, sai ki kwanta da murya ki shagwabance, “dan Allah wane ni ina son abu kaza” irin haka dai.

Shagwaba na sanya maza annashuwa, kuma zuciyarsu na yin fari, kai hatta farin cikinsu ma karuwa ya ke. In ko a kan gadon barci ne, wani irin tsagwaron sonki ne zai na haurowa cikin zuciyar mijinki.

Hanyoyin Yin Shagwaba Ga Namiji

  1. Ki yi iya kokarinki wurin mayar da mijinki abokinki domin zai kara saki jiki da ke fiye da yadda kike tsammani.
  2. In son samu ne, lokaci zuwa lokaci ki kasance kamar wata yar karamar yarinya a wurinsa wurin shagwaba.
  3. Wataran haka kurum in ana cikin nishadi ki ce masa ya goya ki (fatan dai ba za ki yi wahalar dauka ba, shi yasa nake shawartar mata da su rinka motsa jiki).
  4. In ko yana zaune cikin nishadi ko normal mood, ki shigo wurinsa sai ki zauna, “ki hada ido da shi, ki yi masa murmushi, in ya maido miki ki dan murguda masa baki ki yi dariya ki kwanta a kirjinsa.”
  5. In kin fahimci a normal mood yake kuna hirar nishadi, ki dan rinka yi masa tambayoyi irin na yara domin dauke masa kewa.
  6. Ranar da mijinki yake free, ya ke zaune a gida, bayan kin yi wanka in dai yana mai bedroom ko falo ki ce masa sweetheart ka min kwalliya yau mana, sai ki fada cikin irin marairacewar murya yadda dole sai ya yi miki.
  7. Haka kurum, baby ki hau kan cinyar sweetynki ki yi kwanciyar tamkar wata ‘yar karamar yarinya amma fa in da son samu ne ki na dan hada ido da shi from time to time.
  8. In zai fita kasuwa ko wani wuri, ki rike masa jaka ki raka shi, in za ku rabu ki dan kyakkyabe fuska irin ke baki son ya fitan nan sa’annan ki yi masa addu’a.
  9. In kuna zaune a falo bakwa yin komai ki ce masa ya karanta muku littafin soyayya ko kuma ya yi miki tatsuniya yadda za ku debe wa kanku kewa

Shagwabar Kallo Da Motsi

Domin yin nasarar jan hankalin mikinki, yana da matukar muhimmanci ki iya kallo, ba fa ina nufin ki yi wa mijinki duru-duru da idanu kamar na tsohuwar mayya ba, a’a.

In kin fahimci fari na sanya mijinki murmushi ki dan rinka yi masa shi amma fa ba kowanne lokaci ba, in ko mayataccen kallon sha’awa shi mijinki ke bala’in so, shi ma ki rinka yi masa.

Wasu mazan suna son in suna tare da mace to ta rinka musu mayataccen kallo, ba fa kallon raini ba, kuma ta dan rinka lumshe idanu wa shi.

In ko kika fahimci babu abinda mijinki yafi so sama da kina motsawa a gabansa jikinki na rawa, in zaki zuba masa ruwa yana kallon nonuwanki yayin da kuka sarke idanuwa to hakan ya kamata ki rinka yi masa.

Ko ma dai menene, ki san wacce irin kissa mijinki ke so, walau ta kallo ko ta motsa jiki domin ki cigaba da sanya mishi tunaninki a cikin zuciyarsa yadda da gaggawa babu wata diya da za ta yi miki wuffa da shi.

Shagwabar Tafiya

Shan maganin karin kiba domin ki zama ‘yar lukuta jikinki ya yi nama ko ta ko ina ki rinka zarya gaban mijinki yana kallonki kin yi ragwazozo ba shi ne mafita ba.

Ki na motsa jiki yadda za ki samu damar fito da dukkanin shape dinki su tsaya su dire.

In kin fahimci daga ke sai oganki, abinda ya fi dacewa da ke shine; ki rinka yin tafiya kina motsa dukkanin sauran sassan jikin musamman mazaunanki in har kin fahimci su suke dauke masa hankali kuma yana son taba su ko kallonsu.

In ko ki ka fahimci shi yafi son ya ga nonuwanki a tsaitsaye, to sai ki dage wurin saka bra din da za ta sanya su mikewa, kina dan gantsaro masa kirji yayin da kuke tare za ki ga hankalinsa na kan mutanen,

Ita fa shagwaba ba fa iya kwantar da murya da sauransu ba ne, akwai shagwaba yayin kwanciya da iyali da sauransu.

Ina ma ina da isasshen lokaci na yi miki  bayani a kan wasu abubuwan, amma duk da haka nan gaba za mu kara haduwa da yardar Allah.

Kammalawa

Yau, a cikin rubutun nan mun yi nasarar yin jawabi dalla-dalla game da shagwaba da kuma yadda ake yinta. Mecece ita kanta shagwabar kai har ma da nau’ikanta. A karshe kuma muka baku shawarwari da suggestions akan ita wagga shagwaba.

Muna fatan kun amfana da wannan rubutu, kada ku manta ku yi mana addu’a da fatan alkhairi a rayuwa. Muna gode.

Previous News Next News