Mafi akasarin gurbatattun shuwagabannin siyasar nan tamu a kakar zaben nan ta bana, a zaben shugaban kasa, sanatoci da kuma ya majalissu ba su kawo akwatunansu ba.
Ina tunanin wannan dalilin ya sa jami’ar waka, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya takarkare ya saki sabuwar waka mai taken, “Girmanka Akwatunka”.
Kur’anin Allah wakar nan ta yi masifaffen dan karen dadi, kuma babu adawa ina da yakinin za ku ji dadin sauketa tare da sauraronta.
Domin ya yi ruwan baituka na Allah tsine uwar mai karya cikin wakar nan, abin ba a cewa komai sai a yi kurum.
Haka kuma ina da tabbaci hadi da yakinin cewa dukkanin masoyansa za su so sauraron wagga waka, kai har ma da makiyansa.
Kamar yadda na garzaya shafin HausaLoaded na gano; ashe mutumin ya yi wakar nan ne karkashin jam’iyyar APC shiyyar jihar Kano.
In ba ku manta ba, kafin wannan lokaci da har sun raba hanya da Gwamnan Kano na yanzu wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje inda su ka yi baram baram.
Har ya yi waka ya bai wa Ganduje wuta, cikinta ya ce; kace a cire sunana wannan na ji. Dama ban ce a sakani ba wannan kaji.
Ina tunanin a wata waka da ya yi wa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fadi waccen magana.
To, ko ma dai menene, sai ku sauke wakar nan yanzu, kuma kai tsaye daga shafin SeeyBlog.
Kammalawa
Allah ya kara wa Annabi Daraja, kada kuma ku manta ku cigaba da ziyartar wannan blog domin samun ingantattun sabbin wakokin Hausa.