Tarihin Umar M. Shareef (Mawaki, Jarumi Kuma Mai Shirya Finafinan Hausa)

Umar M. Shareef

Tarihi musamman na manyan Arewa, da fitattun jaruman finafinai da mawakan Hausa abu ne mai matukar muhimmancin da bai kamata mu yi tsallen albarka mu watsarshi ba.

Bisa wannan dalilin na ga ya matukar dace na rubuta kammalalle kuma cikakken tarihin daya daga cikin mawakan Hausa, wato Umar M. Shareef a cikin wannan mujalla ta yau.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

To, ina yi muku lale marhaban da zuwa shafin SeeyBlog, shafin intanit mai albarka da ke kawo muku abubuwa masu muhimmanci a rubutu bayan an yi dogon nazari da bincike a kansu.

Duk wani matashi a Arewacin Najeriya (Arewa) ina da yakini hadi da tabbacin cewa ya san Umar M. Shareef mai wakar Bako, Mariya, Hafeez da sauransu kuma ko ina ya bullo zai iya gane shi.

Sai dai ko waye shi wannan Umar din?

Abinda za ku sani a cikin rubutun nan kenan.

Waye Umar M. Shareef

Umar Muhammad Shareef wanda aka fi sani da Umar M. Shareef fitaccen mawakin soyayya ne (nanaye), jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood kuma mai shirya finafinan Hausa.

An haifi Umar a garin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna a shekarar 1987.

Ya jima yana yin wakokin soyayya, domin kamar yadda ya bayyana a shekarun da suka gabata, ya yi wakoki akalla 600 kuma tun shekarar 2007 taurarinsa suka fara haskawa.

Umar ya yi shura hadi da shahara a kasar Najeriya da ma sauran kasashen Afrika ta yamma. 

Mahaifansa

Marigayi Malam Muhammad Shareef shi ne mahaifin Umar M. Shareef, sannan a shekara ta 2020 Allah ya yi masa rasuwa. Sai dai kawo zuwa yanzu ba mu da bayani game da sunan mahaifiyarsa wacce yanzu haka tana nan a raye.

Karatunsa

Ya yi makarantar firamare da sakadire a garin Rigasa, sannan ya fara karatun Qur’ani tun kafin ya shiga makarantar firamre. Har ila yau yanzu haka ya kammala digirinsa a jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Shekarunsa Nawa Yanzu

In muka yi lissafi za mu ga yanzu haka shekarun mawaki Umar M. Shareef daidai har 36 a duniya. Kuma a shekara mai zuwa 2024 zai cika shekaru 37 a duniya.

Iyalinsa

Matar mawaki Umar M. Shareef sunanta Maryam kuma sun jima a tare har ma Allah (S.W.T.) ya albarkacesu da samun zuriya da ita. Wato sun haifi ‘ya‘ya tare. 

Daga cikin ‘ya‘yansu akwai; Aliyu da kuma Hafsat. Kawo zuwa yanzu ba mu da masaniya a kan ko ya kara samun karuwar wasu ‘ya‘yan ko akasin haka.

‘Yan'uwansa

Bayan ya yi gagarumar nasara a fannin zama mawaki, mai shirya finafinai da kuma jarumin finafinai, Umar M. Shareef ya jawo ‘yan‘uwansa zuwa cikin harkar fim, kuma wanda ya yi fice shi ne kaninsa Abdul M. Shareef. Sai kuma autansu Mustapha M. Shareef.

Kun ji wannan kenan.

Yaushe Ya Fara Waka

Ba kasafai ake samun abinda mutum zai ce yau ya fara shi ba tare da wasu dalilai ba, wasu fushi, wasu soyaya, wasu matsin lambar rayuwa da sauransu.

To, ko ya lamarin ya ke ga Umar?

Umar M. Shareef ya fara waka ne dalilin soyayyar bari daya wacce a turance ake kiranta da one-sided love.

Ga labarin a takaice; akwai wata yarinya da Allah ya jarabceshi da sonta, amma kuma ya gaza sanar da ita, ya kan je gidansu ya yi mata sallama, amma da ta fito sai ya buya ta gama dube-dubenta ba za ta ga bakonta ba har ta gaji ta koma gida.

Ya yi haka har sau uku, rannan sai ya yi kundumbala ya ce, yau sai ya ture wa buzu nadi, ya je gidansu ya yi sallama amma sai aka samu akasi ta ki ta fito, da ya gaji da jira sai ya kawo hanya ya yiwo gida, to a hanyarsa ta zuwa gida ya fara waka har ya isa gida.

Wannan shi ne dalilin fara wakarsa. Wani mawaki mai suna Ibrahim Sulaiman (Zaki) shi ne ya fayyacewa Umar dukkanin kabli da ba’adin waka, kai shi ne ma ya gyara masa dam dama daga cikin wakokinsa na farko.

Haka kuma ya fuskanci kalubalalluka masu tarin yawa, daga ciki akwai kin yarjewar mahaifansa. Wadda da kyar da sidin goshi suka amince masa tare da sa wa abin albarka bayan sun ga wakar ya ke amma kuma bai saki irin tarbiyyar da suka bashi ba ya kama wata bare.

Taurarinsa sun fara haskawa ne a shekarar 2007, kuma sun ci gaba da haskawa har zuwa yau, domin ya yi wakoki irin daban-dabam kamar na soyayya, biki, siyasa da sauransu.

Wasu Daga Cikin Wakokinsa

Ga wasu nan daga cikin shahararrun wakokin Umar nan mun kawo muku. Duk da cewa mawakin ya yi wakoki sama da 600 daga farkon fara wakarsa zuwa yau, amma ga wadanda muka dan zakulo nan daga tsoffin wakokinsa wadanda suka shahara sosai.

  • Bako
  • Sareena
  • Jirginso
  • Jinin jikina
  • Ruwan dare
  • Zainabu Abu
  • Kar Ki Manta Dani
  • Hafiz
  • Ciwon idanuna
  • Arewa
  • Ciwon so
  • Mariya
  • Wazana ba kaina da sauransu.

Sabbin Wakokinsa

Daga cikin sabbin wakokinsa akwai irin su;

  • Rike
  • Zuciya
  • Nafada
  • Kan Kauna
  • Rayuwata
  • Hawayenki
  • Na Yarda Dake
  • Babban Rana
  • Ki Bani Soyayya da sauransu.

Kundin Wakoki (Albums)

Umar ya yi albums da dama wadanda suka hadar da;

  • Masoya – 2016
  • Tsintuwa – 2016
  • Kalaman Bakina – 2017 
  • Babbar Yarinya – 2017
  • Kuyi Hakuri – 2017
  • Ni Da Ke – 2018
  • Bako – 2018
  • Fati – 2021
  • Zainabu Abu – 2021
  • Farin Jini –  2022

Hadaka a Fagen Waka

Mawaki Umar M. Shareef ya yi hadaka da mawaka da dama a cikin wakoki mabambanta kamar su mawaki;

  • Nura M. Inuwa
  • Adam A. Zango
  • Hamisu Breaker
  • Abdul D. One
  • Lilin Baba da sauransu

Finafinan da ya Fito

A baya mun bayyana muku cewa; Umar ya kasance jarumin finafinan Hausa, kwarai haka ne domin ya fito a cikin finafinai irin su;

  • Mujadala
  • Sareena
  • Mansur
  • Mariya
  • Hafeez
  • Fati
  • Ciwon Idanuna
  • Karki Manta Dani
  • Zainabu Abu
  • Tsakanin Mu da sauransu.

Finafinan da ya Shirya

Mafi akasarin finafinan da Umar ya fito a karkashin kamfanin Ali Nuhu, FKD Production ya fito. Amma kuma akwai finafinan da ya shirya shi ma karkashin kamfaninsa mai suna Shareef Studio.

Finafinan su ne;

  • Jinin Jikina
  • Zarah

Karramawa

Ya karbi kyaututtuka da karramawowi da dama daga kungiyoyi da dama kamar su;

  • Kannywood films award
  • Afrikan actors

Tambayoyi Masu Alaka

Tarahin umar m shareef, tarihin umar m shareef, tarihin abdul m shareef, http //tarihin umar m shareef, takaitaccen tarihin umar m shareef, tarihin jarumi umar m shareef, bbc hausa tarihin umar m shareef, cikakken tarihin mawaki umar m shareef, cikakken tarihin umar m shareef.

Previous News Next News