Ina yi wa duk wanda ya samu damar ziyartar shafin nan barka da zuwa. Fatan Allah ya amfanar da mu abinda za mu rubuta mu karanta.
{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}
Yau, za mu yi bayani ne a kan yadda ake wankan janaba, juma’a, biki da haila da sauransu.
Sai dai kuma za mu karkatar da hankalinmu ne dungurungun ga wankan janaba domin dalili guda.
Dalilin kuwa shine; abinda ya bambanta wankan juma’a, janaba, biki, idi da haila niyya ce.
Lokacin da za ka fara wankanka niyya ce kadai ke bambanta wanne irin wanka kake son yi.
Amma yadda ake yinsu duk daya ne.
Mecece Janaba
dai kamar yadda duk wani baligi mai hankali ya sani ana samunta ne ta hanyoyi da dama; ta hanyar fitar da ruwan maniyyi daga zakari ko farji walau ta fannin saduwa ko akasin haka.
Wankan Haila
Jinin haila ko mu kirashi da jinin al’ada, wani jini ne da mata kan yi lokaci-lokaci. Kuma ana yi masa wanka kamar yadda ake yi wa janaba wanka. Shi ma wankansa iri daya ne da na janaba, niyya ce kawai ta bambantasu.
Wankan Biki
Shi kuma wanka ne wanda mata ke yinsa bayan sun haihu. Kazalika shi ma niyya ce kawai ta bambanta yadda ake yinsa da sauran wankakkakin.
Wankan Idi
Walau na babbar Sallah ko Karama. Shi ma wanka ne wanda ake yinsa yayin da za a tafi hawan Idi. Niyya ce kawai ta bambantashi da sauran.
Wankan Juma’a
Wanka ne da ake yinsa kowacce ranar juma’a idan za a tafi masallaci domin gudanar da sallar juma’a. Kuma shi ma niyya ce kawai ta bambantashi da wankan janaba.
Nau’ikan wankan dai kam suna da ‘dan yawa, to amma duk nau’i daya ake yinsu. In har ka iya wankan juma’a to ka iya na janaba, in kika iya na haila to kin iya kowanne. Haka lamarin ya ke.
Kamar dai yadda na fada a baya, zan kara tunasar da mu, niyya ce kadai ke bambanta kowanne irin wanka musamman irin wannan na ibada, ba fa wankan dauda ba.
Yanzu za mu shiga cikin asalin jawabin.
Wajibcin Wankan Janaba
Ba fa ni na fada ba, Allah Madaukakin Sarki ne ya fada a cikin Suratul Ma’ida, Aya ta 6, inda ya ce, “Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi wanka.”
Haka ma a wani hadisi wanda Abu Dawud ya ruwaito, Manzon Tsira, Muhammadu (S.A.W) ya yi fadi ga Sayyadi Aliyu (R.A) inda ya ce, “Idan ka fitar da ruwa to ka yi wanka.”
Saboda haka idan muka yi duba na fahimta, duba na hankali ga wannan umarni guda biyu, na Allah da Manzonsa, to lallai sai mu hakikance wankan janaba ya zama wajibi ga dukkanin musulmi. Wajibi ne.
Yadda Ake Wankan Janaba
A nan, za mu dauki fatawar marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam mu yi amfani da ita. Kamar yadda malam ya ce, wankan janaba ya siffantu gida biyu; akwai Siffatul Ijza (wato Siffar Wadata) sannan akwai Siffatul Kamal (wato Siffar Kamala).
To, wadannan siffofi za mu kawo yadda ake yin wankansu daki-daki, domin saukin fahimta.
Wankan Janaba a Siffar Kamala
Da fari ka fara samu ruwa mai tsarki tukunna ka cika butarka ko ka zuba a mazubin ruwanka.
Sai ka tafi makewayi (bandaki), kada ka manta ka yi addu’ar shiga bandakin, sannan ka shiga da kafar dama.
Bayan ka shiga, sai ka karkato da bakin mazubin ruwanka ka wanke hannayenka sau uku. Sannan sai ka tsoma hannu a ruwan ka debo ka wanke gabanka. In buta ce ka tsiyaya. Hakika aiki ba ya yiwuwa sai da niyya, to kulla niyya ma a nan fararun ne. A daidai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin za ka kulla niyya (walau ta janaba, haila, biki, idi da sauransu. Amma fa a zuci ake kulla niyyar).
To, daga nan sai ka yi alwala irin yadda ka ke yin alwala idan za ka yi sallah, komai kake yi a alwalar sallah to ka yi. Abu daya ne kawai ban da shi; wato wanke kafafu, wannan ka kyaleshi daga karshe ake yinsa.
Abu na gaba, sai ka jika ko ka tsoma hannayenka guda biyu a ruwan ba tare da ka debo ba, sannan ka murmurza kanka. Ana yin haka ne domin laimar ta taba kowanne gashi na kanka, domin yayin da maniyyi ke kokarin fita daga jikin ‘dan adam kowanne gashi budewa ya ke yi.
Bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannunka na dama ka zuba a kanka, ka tabbatar ya game ko ina. Ka yi haka har sau uku.
To, idan ka yi haka sai ka debi ruwa ka game ko ina na jikinka da shi, amma ka fara da bangaren dama kafin na haggu. Ka kuma tabbatar ya taba ko ina.
A karshe, sai ka wanke kafarka ta dama, sannan ka wanke ta hagu. Bayan ka maida tufafinka sai ka fito da kafar dama tare da yin addu’ar fitowa daga bandaki. Shi kenan ka gama wankan janaba a kamalarsa.
Alhamdulillah.
Yanzu kam mun kammala da yadda ake yin wankan janaba a siffarsa ta kamala, sai mu karasa zuwa wankan janaba a siffarsa ta wadata.
Kun kuwa sani, in aka ce wadata, to fa wadatar ake nufi, saboda haka muje zuwa.
Wankan Janaba a Siffar Wadata
Ni kaina na fi son siffar wadatar nan, domin ya fi sauki. Ba stress, kuma dama shi dama addinin musulunci saukakken addini ne. Kuma dalilin da ya sa wannan wankan ya fi sauki shi ne; saboda shi ba a bukatar ka yi alwala yayin gabatar da wankanka.
Ga yadda ake yinsa.
Ka samu ruwa mai tsarki, ka tafi bandaki, kada ka manta ka yi addu’ar shiga bandaki sannan ka shiga da kafar dama.
Ka na cire tufafinka, sai ka yi niyyar yin wankan, sannan ka dauki ruwan ka watsa a jikinka ya game ko ina. In kuma a kogi, rafi ko swimming pool ne sai ka yi tsalle ka fada ciki bundum. Dama ka riga da ka kulla niyyarka kafin ka shiga.
Ka na fitowa abu biyu za ka yi. Na farko; kurkurar baki. Na biyu; shaka ruwa a hanci da fyacewa. Ka na yin haka, shi kenan ka kamalla wankanka na janaba, idi, haila, biki da sauransu.
Kuma ya halatta ka yi sallah da wagga wanka. Kuma hadisi cikin Sahihul Muslim ya nuna haka. Sai dai wanda ya yi na farkon ya fi ka cikar kamala da lada saboda ya bi dukkan sharuddan wankan.
‘Dan‘uwa, wankan janaba a siffar wadata ya fi sauki matuka, kawai bambancin shi ne; wanda ya yi na farko wankansa ya fi naka cikar kamala kuma zai fika lada.
Saboda haka a shawarce ka rike na farkon sosai, in kuma a halin ujila kake to sai ka yi na biyun. Wannan shawarace na baka, ba daga cikin rubutun ya ke ba.
Kun san an ce; “ka so wa ‘dan‘uwanka abinda ka so wa kanka.” Ni ma na fi ganin saukin wankan mai suffar wadata, amma na fi yin mai suffar kamala wallahi.
Tunasarwa
Gaba daya nau’ikan wankan nan biyu, kowannensu za ku iya yinsa a matsayin wankan IDI, Juma’a, Haila, Biki da sauransu. Na kara tunatar da mu, niyya ce kawai ta bambantasu. Amma yadda ake wankan iri daya ne sak.
Abinda na kuskure a ciki Allah ya gafarta min, amma na yi iyaka kokarina wurin warware bayanin wankan kamar yadda marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya yi bayani.
Tamat.
Tambayoyi Masu Alaka
Wankan Janaba, Wankan Janaba Sheikh Jafar, Wankan janaba PDF, Wankan Janaba Audio, Wankan Janaba na Mata, Wankan Janaba Kala Nawane, Wankan janaba a Musulunci, Bayani Akan Wankan janaba. Wankan Idi, Wankan Sallar Idi, Yaya Ake Wankan Idi, Yadda Ake Wankan Idi. Wankan Haila, Niyyar Wankan Haila, Siffar Wankan Haila, Wankan Haila a Musulunci. Wankan Biki. Wankan Juma’a, Yaya Ake Wankan Juma’a, Yadda Ake Wankan Juma’a.