Cikin fuskar rahama na ke yi maka barka da zuwa shafin nan mai albarka na SeeyBlog.
Yau, za mu tattauna ne a kan wadansu hanyoyi guda 6 da za ka bi domin samun Adsense Approval a sabon shafinka na yanar gizo cikin sauki.
Na kudurci niyyar yin rubutun nan sakamakon da dama daga cikin abokai musamman masu ikirarin su ne Arewa Bloggers suna yawan kawomin korafin kasa samun Adsense approval a blogs nasu.
Bisa wannan dalili, yasa naga ya dace na wallafa salo da kuma dabarun da nake amfani da su wajen samun adsense approval hankali kwance.
{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}
Amma fa ku sani, komai sai da yardar Allah ya ke tabbata, ba salo da dabaru kadai kake bukata ba kafin ka samu adsense approval.
Ya kamata ka dan rinka gaurayawa da addu'a, kunsan ita maganin masifa ce, kuma katangar karfe ga daukacin musulmi.
Duba da yadda Adsense suka canza policy dinsu na 2020, 2021 da 2022 to samun approval a shafin Hausa zai yi wuya, saboda wasu na ikirarin wai Hausa Language ba recogniseable language bane world wide.
To, amma fa ni a irin nawa tunanin babu abinda zai hana Google Adsense su yi monetizing na blog dinka domin na samu approval 2020, 2021, 2022 ga kuma na 2023 ma suna kan hanya.
Abubuwa 6 Da Zaka Kiyaye
Domin takaita tsayin rubutun bari na fada maka wasu abubuwa guda shida da za ka kiyaye domin samun Adsense approval a shafinka da ka bude.
- Ka yi amfani da template mai kyau a shafinka
- Ka yi posts masu rubutu da yawa (enough contents per page) a shafinka
- Ka saka about, contact, privacy policy da dmca pages a shafinka
- Ka yi posts masu kyau, banda satar post din wasu shafukan wato (plagiarism)
- Ka yi amfani da original photos, banda copyright graphics
- Ka tabbatar shafinka yana samun ingantaccen traffic (in son samu ne ma organic traffic)
- Kada ka yi post din batsa, makamai da sauran illegal contents a shafinka.
Ko wanne abu da na fada a wannan jeri zan maka bayani dalla-dalla akansa, fatan zai amfaneka.
Ka yi Amfani da Template Mai Kyau a Shafinka
Samun Adsense approval bai danganta da blogging platform din da kake ba, walau Blogger ko Wordpress, kawai kana bukatar template mai kyau.
In fa nace ma template mai kyau ina nufin; wanda ya ke da design mai kyau, kuma yake navigation theme, bi ma’ana wanda zai ba wa maziyarci damar karade shafinka da duba posts masu alaka (related posts da next and previous posts da kuma breadcrumb) cikin sauki.
Ba na tunanin za ka samu adsense approval da wani jigari-jigarin template a blog dinka, kana bukatar responsive da good looking template.
Wasu suna amfani da free templates, amma fa a shawarce ku nemi premium templates ku dora a shafinku.
Kuma ku tsara shi yadda ya kamata, hakan zai bada gudunmawa sosai wajen samun adsense approval a shafukanku.
Sannan, ya kasance template din baya da nauyi, ma'ana yana da speed mai inganci, kuma yana da navigation mai kyau.
Akwai developers da ke samar da ingantattu kuma kyawawan templates na Blogger kamar su templateify. Za ku iya shiga shafinmu domin zabo irin theme din da kuke so.
In a Wordpress ne, ku gwada amfani da Publisher Theme, Genesis, Newspaper da sauransu.
Ka yi Posts Masu Rubutu da Yawa (enough contents per page) a Shafinka
Yin dogo kuma wadaccen rubutu a cikin post wanda ke fayyace komai da komai game da abinda kake tattaunawa na da matukar muhimmanci wurin neman Adsense approval.
Zai kyautu ku rinka post na contents wanda suka fi 500 words. Irin akalla 1000 words, 1400 words, har zuwa 2000 words.
Da yardar Allah za ku samu approval.
Ka Saka About, Contact, Privacy, Disclaimer da Dmca Pages
Yana daga cikin kuskuren da wasu ke dirkawa kenan, ba sa saka about pages a shafukansu suke apply na adsense.
Ba na tunanin za su yi approve na shafinka muddin ba ya da about us, contact us, privacy policy, disclaimer pages in da hali ka hada har da dmca pages.
In dai ka saka musu wadannan pages din, kuma ka saka links dinsu a navigation menu din shafinka, hakan zai kara adadin damar samun adsense approval din shafinka.
Ka yi Post Mai Kyau ban da Satar Post din Wasu (plagiarism)
Ina mamaki ganin yadda wasu ke yin copy paste na post din wasu shafukan zuwa shafukansu.
Ka manta menene blogging ne? Rubutu za ka rinka yi mai amfani, ba wai ka zuba ido kana kallon wani yana wallafa post mai kyau kai kuma kana binsa kana sace masa ba.
In har so kake ka samu karbuwa a wurin google adsense, yana da kyau ka rinka rubuta posts dinka da kanka.
Domin mutane za su so ziyartar shafinka in dai yana da original contents masu daukar hankali da amfani.
Akwai hanya da za ka bi wajen gane ko post din shafinka na wani ne ka sata ko kuma ya satar maka, ta hanyar amfani da shafin copyscape.
Mai karatu indai adsense approval kake so, kawai ka rubuta posts masu amfani, kuma original a shafinka tukunna.
Ka yi Amfani da Original Photos, Ban da Amfani da Copyright Graphics
Kunsan masu iya magana sunce; Marar shi baya zuciya, hakan na nufin domin ka samu shiga a wurin adsense dole za ka bi dokokinsu da fari.
Eh mana, ka na amfani da apps na graphic design irinsu pixellab, picsart, canva da sauransu kana hada graphics din da za ka rinka saka wa a shafinka.
In dai original graphics kake amfani da su, ina da yakinin za ka samu approval cikin sauki da yardar mai sama.
Amma ko da kana da original posts yma graphics din ba original bane, bana da tabbacin za su yi approval din shafinka.
Duk da haka, kunsa abin rabo ne.
Ka Tabbatar Shafinka Yana Samun Ingantaccen Traffic
Wato 'dan uwa babu wani 'dan adam da zai rayu ba tare da abinci ba, don haka babu wani blog da zai ginu ba tare da traffic ba.
Hakan na nufin muddin shafinka baya da makaranta to babu wanda zai ga ads dinka balle ya bude su.
Kuma hakan ya kara nuna cewa shafin bai gama cika sharuddan samun approval ba.
In har kana son adsense approval, kamata yayi ka fara gina shafin, sannan ka nemi adsense.
Kuma organic traffic yafi bada gudunmawa wajen samun approval, amma fa ko babu shi referral ma yana taimakawa sosai.
Bisa wannan dalili, na ke baka shawara lallai ka gina shafin ka yadda ya kamata kafin ka nemi adsense su fara dora masa tallace-tallace.
Kada ka yi Post din Batsa, Makamai da Sauran Illegal Contents
Nan ma kuma anzo inda yafi kai-kai ga arewa bloggers, domin na san da dama daga cikinsu banda sharri da kage ba abinda suka iya.
In kaga wani title din kai ka rantse mala'iki mai daukar rai ba zai ziyarci mutum ba wata rana.
A shawarce: indai so kake ka samu approval na adsense kada ka rinka post din batsa a shafinka, ko na makamai, ko na kayan sata irinsu (cracking, modding) da sauransu.
Ina da yakinin hakan zai taimaka sosai wajen saukaka maka samun adsense approval.
******
Ba a iya nan na so tsayawa ba, amma babu yadda na iya a nan zan karkare wannan rubutu nawa.
Ga masu tambayata, kuma su yi comment a wannan rubutu zan yi iya kokari na wajen ganin na basu sahihiyar amsa.
Duk mai neman approval ina masa fatan nasara, Allah yasa a dace ameen.