]Tir fa kashi!
Wai!
Ilimi dai masu iya magana suka ce kogi ne, mai zurfin da ya wuce zurfin tunanin mutum. Duk iya kwankwadar da ka yi masa, sai ka gama yinka za ka ga ashe kai cokali guda ma ka sha.
Yau, ina cikin bincike akan abinda ya kamata na yi muku rubutu akansa, sai kawai na ci karo da wagga tambaya, “amfanin shan nonon mace ga lafiyarta”.
Allah Sarki ni, ai ni a zatona, shan ruwan nono mace ga jariri muka san shi, wai ashe likitoci su sun jima da wuce wurin a bincike-bincikensu.
Lafiya dai kam uwar jiki ce, babu kuma mai fushi da ita, bisa wannan dalili zan yi muku bayani karkashin kiwon lafiya yanzu.
{tocify} $title={Table of Contents}
Wadansu kwararru (masana) a fannin kiwon lafiya (wadda ya fi kiwon akuya) sun shawarci mazaje (masu aure) da su rinka shan nonon matansu.
Masanan sun yi wannan kira ne a cikin wani shiri da aka bullo da shi saboda a wayar da kan mutane dangane da illar cutar cancer (daji) da kuma breast cancer (kansar mama).
Also Read: Ciwon Ulcer, Alamomin Ciwon Ulcer, Da Hanyoyin Magance Ciwon
A watan shan mama ne dai shugaban kamfanin magunguna na tsirrai na duniya ya yi wannan kira don ya karfafa wa maza gwuiwa su dage wurin shan nonon matansu (walau wadanda suka haihu ko wadanda basu haihu ba).
Nonon mace dai wata matattara ce a kirjinta wadda ke kunshe da wadansu jijiyoyin kai sakonnin da suke kai wa kwakwalwarta sako da zarar an taba nono ko an sha shi.
Mazaje da dama na matukar sha’awar shan maman matayensu, kamar yadda su kansu matan ke bala’in sha’awar a sha musu mamansu musamman lokacin kwanciyar aure.
To, sai dai wadansu mazajen na yin iyaka da shan nonon matansu da zarar sun fahimci matar ta dauki ciki ko kuma ta haihu saboda su a tunaninsu shi wannan ruwan nonon na da illa ga manyan mutane.
Sai dai binciken masana ya yi fatali da wannan tunani na mafiya mazaje, domin kuwa kamar yadda ruwan nonon mace ke kara wa jarirai karfin garkuwar jikinsu to haka yake kara wa manya.
Don haka, a zahirce ba wai don iya kadai jarirai Allah ya halicce nonon mace ba, har ma da manya.
Bugu-da-kari, kamar yadda shan nonon mace ke da matukar amfani ga ‘da namiji bayan jariri, to haka su ma mata yake da matukar muhimmanci a rinka sha musu nononsu.
Kada ka musa maganar nan da muka kawo maka domin dauke muke da tarin hujjoji har guda bakwai wadanda muka samu daga wurin masana binciken kiwon lafiya
Ba abin kunya bane don ka yi sokoko kana shan nonon matarka, domin da ka san alfanun shi wannan shan nonon ga lafiyarka da ba ka gajiya da yin shi ba.
Kada na cika ku da surutu, ga alfanun shan mama ga mace nan guda hudu sai kuma na maza su ma da za mu kawo.
Amfanin Shan Nono Ga Mace
Bayan jin dadi akwai kuma wadansu fa’idoji na lafiya da shan nonon mace ke da shi wa jikinta.
Daga cikinsu akwai;
Inganta Lafiyar Zuciyar Mace
Na tabbata da dama daga cikin mazaje ba su san cewa shan nonon matayensu na da matukar alfanu ga lafiyar zuciyoyin matansu ba a likitance.
To, in ba ku sani ba, shan nonon mace na taimaka wa kofofin numfashinta kwarai da gaske.
In har aka sha wa mace nononta na dogon lokaci, to bugun zuciyarta na karuwa fiye da yadda yake asali, yana kai wa 110 a minti daya.
Wannan saurin bugun zuciyar tata, tamkar wani sabon samfurin motsa jikin jijiyar zuciyar ne domin ta kara lafiya.
Cikowar Fuska da Washewarta
Gareku ‘yan‘uwa mata; duk wacce ke son fuskarta ta washe ta saki cikn cikakken nishadi kuma fatarta ta washe to ta tabbatar mijinta na sha mata nonota.
In ya manta ma, ki tuna masa, domin ke abin zai fi amfana fiye da shi.
In dai ana sha wa mace nononta, to hakan zai taimaka wajen bunkasa tsokar da ke fuskarki sanna zai inganta lafiyar kewayarwar jini a fatarki.
In har isasshen jini na kewaya fatar mace, hakan na sanya fatar ta washe.
Bugu-da-kari, ga mace da ba ta sha’awar jima’i, akwai magani ba tare da kin bi masu maganin gargajiya ba.
In har mijinki ya zo miki da bukata ke kuma ba kya sha’awar saduwar, ki fara bashi shawarar ya fara da shan mamanki, za ki ji ki sha’awarki ta taso.
Kara Karfin Garkuwa Jiki
Kowa dai ya san cutar kanjamau wacce ke yin raga-raga da garkuwar jiki. To amma shi shan maman mace magani ne sahihi da ke matukar kara wa ita garkuwar jikin mace karfin samar da isassun kwayoyin yaki da kwayyoyin cuta.
Duk lokacin da namiji ne sha wa mace mama, ko kun san cewa numfashinta na karuwa ne da bugu sittin (60) a kowanne minti?
Haka kuma yayin da ake sha mata maman, dole za ta rinka shakar iska yana fitar da ita da-sauri da-sauri, to, hakan na magance cututtuka da dama da suka danganci hunhu.
Takaita Yiwuwar Cutar Daji ta Kama Mace
Kamar yadda binciken masa ya tabbatar; duk macen da ake yawan shan mamanta kuma ake yawan lallatsa shi to hakan na taimakawa wajen kamuwa da matsalar kumburi.
Shi kuma wannan kumburin mafi yawancin lokuta shi yake rikidewa zuwa cutar dajin mama.
Yayin da ake lallatsa nonon mace kuma ake shansa da tsotsarsa hakan na kara yawaitar zirga-zirgar homon da hana kumburinsa.
Amfanin Shan Nonon Mace ga Namiji
Masu binciken lafiya sun tabbatar da cewa, yadda ruwan nonon mace ke da alfanu a jikin yara haka ya ke a jikin manya.
Ga wasu daga cikin fa’idojin shan nasa ga maza manya;
- Yana hana maza kamuwa da cutar daji
- Yana taimaka musu wurin saurin narkewar abincin da suka ci a cikinsu
- Yana karfafa musu garkuwar jikinsu.
Shawara ga Mace
‘Yar‘uwa, a matsayinki na mace wadda ke shayarwa, duk lokacin da maigidanki ya bukaci shan mamanki kada ki hana shi domin shi ma yana taimaka masa.
In kuma kika yi duba zuwa rubutun da ke sama, za ki ga na kawo fa’idojin shan mamanki ga mijinki.
Har-ila-yau, manyan mutane de fama da cutar daji, ko matsalar narkewar abinci a cikinsu, ko kuma garkuwar jikinsu ta yi rauni, to a asibitoci ana shawartarsu ne da su juri shan nono ko madara domin rage irin wannan matsala.
Allah ya sa mu dace.