Illar Zama ba Tare da Jima'i ba na Tsawon Lokaci (Ga Budurwa)

Budurwa

Budurci shine mace ta kama kanta ba tare da yin Jima'i ba har sai bayan tayi aure. 

Macen da bata taba sanin namiji ba itace wacce a Hausa ake kiranta budurwa.

Duk wata 'ya mace burin ta ta shiga gidan mijinta a budurwa. Duk wani namiji burinsa ya auri budurwa.

Haka suma iyaye musamman masu aurar da mace, abun alfahar ne a wajensu su aurar da 'yarsu a budurwa.

Sai dai wannan budurcin da ake son kasancewa da shi da kuma alfahari da shi, yana iya yiwa mace illa har ma da maza idan ya dauki lokaci mai yawa ba a kawar dashi ba. 

Wannan yasa iyaye musamman irin na dori suke saurin aurar da yaransu mata da karancin shekaru. 

Hakan ne ma yasa idan mace ta haura wasu shekaru ba tare da yin aure ba ake mata kallon ba budurwa bace.

Macen data dauki lokaci mai tsawo cikin budurci martabarta da darajarta yakan zube duk da kuwa bata taba sanin namiji ba. 

Haka nan macen data san namiji komai karancin shekaru ta tana fin wacce batasan namiji ba saurin fahimta da budewar kwakwaluwa.

Ita macen da aka mata aure da wuri mahaifarta yana saurin ajiye da da kenkensarsa cikin sauki fiye  da macen data jima da budurci. 

Ko a wajen haihuwa ita macen data samu yin aure da wuri tana samun saukin yin nakuda fiye da macen data jima cikin budurci.

Macen da aka kawarwa budurci da wuri tafi wacce ta jima da budurci jin dadin kwanciyar aure.

Sai dai wannan darasin ba wai yana yiwa matan da basu samun yin aure da wuri bane shagube. 

Illa kawai darasin na magana ne akan matan da suke samun daman yin aure tun suna da kuruciya amma suke sakaci da yin hakan. 

Darasin na magana ne akan tasirin da alfanun rike budurci kamin aure. Da fatan matan da suke burin yin aure Allah Ya basu mazajen auren nasu.

Su kuma marasa aure ya basu ikon rike budurcin nasu. Wadanda kuma suka rasa budurcin su ba ta hanyar aure ta fyde, yaudara da asiri. Allah Ya bi musu hakkin su.

Su kuma wadanda suka rasa budurcinsu ta hanyar kwadiyin bura, kudi ko soyayya. Allah Ya yafe musu idan sun nemi gafararsa suka tuba.

Allah ya saka wa Malamin Tsangayar Tonga da alkhairi, za ku iya bibiyarsa ta shafin sada zumunta na Facebok.

Previous News Next News