Kwankwaso | Sunusi | Abba Gida-Gida |
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce gwamnati mai zuwa a Kano za ta sake duba batun tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.
Sanusi wanda ya zama sarki a wa’adin karshe na Kwankwaso a matsayin gwamna, Gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ne ya tsige shi, wanda shi ne mataimakin gwamna a lokacin da aka nada sarkin.
An cire Sanusi ne a ranar 9 ga Maris, 2020, sannan kuma an kore shi daga Kano aka mai da shi zuwa Loko, wani yanki mai nisa a jihar Nasarawa, yayin da ake binciken kudaden masarautar da ke karkashinsa.
Haka kuma Ganduje ya raba masarautun gida biyar ya nada sarakunan da suka yi daidai.
Sai dai da yake magana a wani faifan bidiyo, Kwankwao ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zababben gwamna, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, zai duba batun tsige sarkin da kafa sabbin masarautun.
“Mun yi yakin neman zabe kuma kamar yadda kuka sani muna da farin jini a Najeriya musamman a jihar Kano, yanzu mun dawo kuma in Allah ya yarda za mu ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatinmu ta bari. Wannan gwamna mai jiran gado da tawagarsa za su dauke su.”
“A matsayinmu na dattawa, za mu ci gaba da ba su shawarar yin abin da ya dace. Mun yi kokarin kada a sa baki a batun kawo ko tsige wani sarki, amma yanzu dama ta zo.
“Wadanda aka bai wa wannan dama za su zauna su duba batutuwan. Za su duba abin da ake sa ran yi. Bayan Sarki, hatta Masarautar ta rabu gida biyar. Duk waɗannan suna buƙatar yin nazari. Galibi shugaba yakan gaji alheri, mummuna da al’amuran da suke da wuyar sulhu”.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya sa Gwamna mai jiran gado ya samu damar tafiyar da al’amura cikin sauki.