Hakika muna da kaso mai tarin yawa na masu karatun litattafan Hausa wadanda aka fi wa lakabi da Hausa Novels. Kuma mafi yawancin makaranta da marubutan irin wadannan litattafai mata ne.
Saboda haka ina jinjina gareku makaranta da kuma marubuta litattafan Hausa novels.
{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}
Baya ga haka, a cikin wannan rubutun na yi iya kokarina wurin tattaro tare da tato wadansu fitattu daga cikin shafukan yanar gizo na hausa novels da muke da su. In dai littafi ki/ka ke bida to kana ziyartar daya daga cikinsu to ka samu kuwa.
Ba ni son cika maziyarcin wannan shafi da surutu na babu gaira balle dalili, saboda haka ga jerin shafukan nan.
1. Gidan Novels | Hausa Novels
Image source: SeeyBlog |
Shararren shafin karanta cikakkun hausa novels ne wanda wani Marubuci kuma mawallafin yanar gizo mai suna Muhammad Abba Gana Kolo ya bude shi tun shekarar 2018.
A cikin shafin za ku iya samun cikakkun litattafai wadanda ba sai kun daukosu a kan wayarku ba in har kuna so ku karanta. Kawai post za ku bude cike da complete littafi.
Tabbas, kawo zuwa yanzu babu wani shahararren shafin karanta cikakkun litattafan Hausa da ya kai Gidan Novels.
2. Taskar Novels
Image source: SeeyBlog |
Matashin shafin dauko cikakkun litattafan hausa novels ne, da litattafan yaki wanda marubuci kuma marubucin yanar gizo Shuraihu Usman ya kirkira.
A kalla akwai fiye da litattafai 2,000 a kan shafin. Kawai shiga za ku yi, ku yi search, ku bude post din sannan ku yi download. Shi kenan.
3. Bankin Hausa Novels
Image source: SeeyBlog |
Bankin hausa novels shafi ne wanda ke dauke da akalla litattafai dubu 3,800. Hakika in dai litattafan hausa novels ka ke so wadanda za ka karanta cikin sauki to kana zuwa bankin hausa novels to kakarka ta yanke saka.
Kazalika, shafin an budeshi ne shekaru hudu da suka gabata. Don haka cike ya ke da litattafai masu armashin gaske.
4. 2gnovels
Image source: SeeyBlog |
Akalla akwai litattafan hausa fiye da guda 3,000 a shafin 2gnovels. Tabbas wannan shafi tumbatse ya ke da litattafan hausa iri-iri.
Shafin 2gNovels shafin yanar gizo ne mai dauke da zallar litattafan hausa. In dai kana son karanta Hausa Novels to kawai ka ziyarci wannan shafi.
Ina da yakinin za ka samu irin littafin da kake so a ciki.
5. Aihausanovels
Image source: SeeyBlog |
Shafi ne wanda ke kawo cikakkun litattafan hausa a text document. Wasu lokutan kuma shafin na kawo litattafai ne a part-part. Misali part 1 to 20.
Aihausanovels ya shahara wajen kawo muku litattafai complete dinsu, kai ba fa iya novels ya tsaya ba. Akwai wasu karin abubuwan. Irinsu labarai, rahotanni, bidiyoyi da sauransu.
Ba fa iya su kenan ba!
Dalilin da yasa na ce haka saboda akwai wasu shafukan na daukowa tare da karanta litattafan hausa novels, to amma ni kaina na fi aminta da wadannan guda biyar din.
In dai abinda ka ke so shi ne hausa novels, to ka ziyarci daya daga cikin shafukan nan guda biyar, tabbas za ka samu abinda ka ke bukata.
Fatan wannan rubutu zai kayatar da kai.
A Kula: Bamu da alhaki, idan har kuka ziyarci daya daga cikin shafukan nan kuka ga sabanin abinda muka rubuta. Ba mu da iko da kansu.