Ina yi muku lale marhaban da zuwa shafin nan namu mai albarka na SeeyBlog.
Yau za mu tattauna ne akan “waye ya fi kowa kudi a Kannywood.” Tambaya ce mai sauki kuma da wuyar amsawa.
To, amma a cikin mujallar yau, za ku ji waye ya fi kowa kudi a masana’anatar shirya finafinai ta Kannywood (walau jarumin fim ko kuma mawaki).
{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}
Cikakken yakini ne da ni akan cewa maziyarcin shafin nan ya san mecece masana’antar Kannywood, amma duk da haka bari mu baku fahimtaccen bayani akanta.
Masana’antar Kannywood
Kannywood dai masana'antar shirya finafinan Hausa ce da ke da babban reshenta a birnin Kano a Najeriya.
Kuma tana daya daga cikin manyan masana'antun shirya finafinai a Najeriya, kazalika ita ce masana'antar shirya fim ta biyu mafi girma a Afirka, bayan Nollywood.
Finafinan Kannywood yawanci ana shirya su ne da harshen Hausa kuma sun shahara a Arewacin Najeriya da kuma tsakanin al’ummar Hausawa a wasu sassan kasar da ma wajen kasar Hausa.
Finafinan Kannywood sun fi mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi al’adun Hausawa da zamantakewarsu, irinsu tarbiyyar iyali, addini, darussan rayuwa, da soyayya da sauransu.
Sau da yawa suna sanya kiɗan gargajiya da na zamani, raye-raye, da suturar gargajiya yayin gabatar da finafinan.
Kuma wannan al’ada a ake nunawa ta shahara a tsakanin masu sauraro da kallon shirye-shiryen waɗanda ke yaba waɗannan abubuwan al'adu.
Masana’antar ta fito da jarumai da dama da masu shirya finafinai da dama a tsawon shekaru, kuma ta bayar da gudunmawa sosai ga harkar finafinan Najeriya baki daya.
Wanda Yafi Kowa Kudi
An jima ana mukabala tsakanin masoyan jarumai da mawakan Kannywood akan waye ya fi kowa kudi, wasu su ce kai wa zai hada kaf ‘yan fim da Sarki Ali Nuhu, Wasu suce Sarkin Waka, Wasu suce Rarara, Wasu su ce Adam Zango.
Wanda Yafi Kowa Kudi a ‘Yan Fim
A bangaren ‘yan fim kamar yadda shafin SarkiLoaded ya bayyana a shekarar 2022 babu wani ‘dan fim da yafi Sarkin Kannywood kudi wato Ali Nuhu Muhamad.
Domin a bisa lissafi da kiyasin da aka gudanar, an gano cewa akalla Jarumi Ali Nuhu na da zunzurutun kudi da kadara na sama da miliyan 150 zuwa 200.
Wanda Yafi Kowa Kudi a Mawaka
Shi ko mutumin da ya dara kowa zunzurutun kudi a cikin kafitanin mawakan Hausa shi ne Dauda Adamu Abdullahi Kahutut Rarara, domin tun daga kan kone masa gida da ofishin da aka yi a jihar Kano ya kamata jama’a ta san cewa in dai Naira ce, to Allah ya amince masa.
A bisa kiyashin da aka gudanar, akalla Dauda Kahutu Rarara yana da arzikin kudi da kadara na sama da naira miliyan 300.
Waye Yafi Kudi a Kannywood
In muka yi duban tsanaki a cikin manyan gwarazan masu arzikin Kannywood din nan guda biyu da muka kawo muku networth dinsu, za mu ga cewa Rarara ya doke Ali Nuhu a kudi nesa ba kusa ba, ya kuma yi masa fintinkau.
Saboda haka a zahirance, overaller na wadanda suka fi kowa kudi a ciki da wajen Kannywood shi ne Dauda Kahutu Rarara dan mutan Katsinan Dikko.
Me Yasa Rarara Yafi Kowa Kudi a Kannywood
Akwai dalilin da yasa Rarara yafi kowa kudi a cikin ‘yan masana’anatar Kannywood.
Dalilin kuwa shi ne; saboda shi mawakin ‘yan siyasa ne kuma ‘yan siyasar kasar nan tamu Najeriya na matukar ji da shi.
Domin kamar yadda muka samu a cikin wadansu ‘yan rade-radi, kafin Rarara ya dodara maka waka a halin yanzu kana da bukatar ajiye masa miliyan 40 a lalace kudin advance kafin ka yi final biya.
Kuma tun da Buhari ya dare mulkin Najeriya, Rarara shi ne shugaban mawakan APC, gashi yana kyautar motoci, wayoyin kece raini, gidaje da kudade da kayan abinci.
Wanda yin hakan in dai mutum hannunsa bai zagaya bayansa ba to ba zai iya yin ko da daya cikin darinsu ba.
Saboda haka a gaskiyar Allah Rarara ya fi kowa kudi a Kannywood, domin yanzu ta proxy ya zama kamar wani shugaba a cikin Kannywood din zai iya cewa ayi ayi, a bari kuma a bari.
Me Yasa Sarkin Waka Ke Wa Rarara Rashin Kunya
Shi duk mutum mai dagawa za ka sameshi da rashin kunya da takama har ma da raina mutane.
Kuma duk cikin abubuwan nan da muka lissafto babu wanda ba hali ne na Yallabai Sarkin Waka ba.
Har ila yau, mafi akasarin masoyan Sarkin Waka sun san cewa akwai digon hassada a cikin zuciyarsa duba da yadda yake ta yi wa Rarara rashin kunya amma shi Rarara din ya share shi ya nuna masa bai kai ya tanka masa ba.
Duk da cewa shi ma Rarara din wasu lokutan bashi da kirki, musamman wurin shagube da cin zarafin ‘duk wanda aka biyashi a kaikaice.
Tom, Allah ya kyauta.