Yadda Ake Gyaran Jikin Amare (Sirrikan Gyaran Amarya)

Gyaran Jiki

Amarsu ‘yar lelen ango, ki fito sannu! 

Babu wacce ta cancanci a yi mata gyara iya gyara, ciki da waje, a yi mata sabis da garambawul kamar sabuwar amaryar da za a kai ta gidan mijinta.

Domin shi sabon ango so yake ya ji amaryarsa zam-zam kamar sabuwar mota, so yake ciki da waje ya ji shi na daban a daren aurensu.

Bisa wannan dalili, sai na fahimci wata irin gagarumar zuzzurfar bukatar sanin yadda ake gyara jikin amarya a kasar Hausa.

{tocify} $title={Table of Contents}

Kuma abin da ya kara bani kwarin gwuiwar yin wannan dogon bayani mai cike da bincike shi ne; mafi akasarin matambayan mata ne.

To, ‘yan uwa mata sai gareku.

Sai dai zan fara ne da yin saukakken bayani akan amarya da kuma nau’ikan amaren kansu.

Wacece Amarya

A kasar Hausa dai, amarya ita ce macen (budurwa ko bazawara) da aka daura aurenta da namiji (walau saurayi ko bazawari) kuma ta ke shirin tarewa ko za a kai ta dakinta.

Nau’ikan Amare

Kuma in har ana maganar amarya ne, to mafi akasin ‘yammata amare an fi amanna da budurwoyi ne wadanda wani namiji bai san su ba.

Su ko zawarawan amare mata ne wadanda aurensu ya mutu da tsoffin mazajensu, sai suka sake aure, za su tare ko suka tare. 

To, dukkaninsu ana ksiransu da amare.

Saboda haka wajibi ne mu yarda cewa nau’in amare biyu ne, akwai budurwoyin amare sannan da zawarawan amare.

Yadda Ake Gyaran Jikin Amare  (Fuska)

In ka dauke kirji (nono), mazaunai da kuma kyakkyawan diri, fuska na daya daga cikin manyan abubuwan da ke dauke wa ‘yam maza hankali, domin kowa na da buri da muradin ganin ya auri mai kyau (ko da me mai ce, Allah ya sawwak).

Ba fa sai kyawunki ya wuce na Sarauniyar Kyawun Najeriya Shatu Garko ba, a’a, kowacce mace kyakkyawa ce.

Amma in dai ke amarya ce yana da kyau ki san yadda za ki gyara tare da tsabtace fuskarki domin fito da tsantsar tsagwon kyawunta.

Hadin Gyaran Fuskar Amarya na Daya

Ki samo wadannan abubuwan da zan lissafto;

  • Man zaitun
  • Kwal da
  • Nono kindirmo (ba fa yoghurt ba)

Yadda Ake Hada Shi

Abu na farko da za ki yi shi ne; ki hada su wuri guda ki gauraya su sannan ki cakuda, sa’annan sai ki na lakata kina shafawa a kan fuskarki.

Bayan kin gama shafe fuskarki, sai ki samu ruwan dumi kina turara fuskarki.

Ina da yakinin za ki sha mamaki in kika ga sakamakon da zai fito dalilin wannan hadin.

Hadin Gyaran Fuskar Amarya na Biyu

Shi wannan da cocumber ake hada shi, kai ba ma hadashi ake yi ba, kawai cocumber za ki samu sai ki yankata kina shafawa a kan fuskarki, za ki ga canji da yardar Allah.

Hadin Gyaran Jikin Amarya

Wallahi tallahi babu wata amarya da ke son jikinta ya kasance ba luwai-luwai gwanin sha’awa ba, kai ba ma iya amarya duk mata haka suke so.

Shi yasa da dama daga cikinsu suke son su yi bulbul, duwawu da nonuwa su fito. To ya ke amarya ga maganin gyaran jiki mun kawo miki wanda zai kara wa jikin abin.

Saboda nace abin ba wai ina nufin matsi ba, a’a, shi ma wannan layinsa daban. Ina yi miki magana ne akan kyawun jiki.

Ku nemi:

  • Daula janna
  • Madarar turare Sultan
  • Madarar turare Kafi-kafi
  • Lalle

Yadda Ake Hada Shi

Da farko dai ku hada su ku kwaba, ko kuma ku jikasu da lallen daga baya ku tace ruwan lallen.

In kuma ba ku son kwabawa kawai ku dafa su, sannan ku tace ruwan lallen, kana daga baya sai ku saka amarya ta rinka wanka da shi.

Sakamakon wankan da take yi da shi, hakan zai sa jikinta ya yi kyau kwarai da gaske. 

Bayan nan sai amarya ta nemi turaren wuta mai kamshin gaske ta rinka turara jikinta da shi.

Kammalawa

Ban so tsayawa haka ba, amma dai a rubutunmu na gaba, zan kawo muku kayan gyara jikin amare na bangaren ni’ima, matsi da sauransu.

A takaice, yau mun tattauna akan yadda ake gyaran jikin amare, gyaran fuskarsu da ma jikinsu baki daya a cikin wagga rubutu.

Allah ya kara wa Annabi daraja.

Previous News Next News