Abubuwa 10 da ya kamata ki sani kafin a yi miki aure - Tsangayar Malam Tonga


Daga Tsangayar Malam Tonga

'Yan mata da dama suna aurene ba tare da an sanar dasu, ko sun nemi sanin wasu abubuwan da yakamata su sansu ba domin inganta zaman aurensu.

{tocify} $title={Table of Contents}

Hakan yasa wasu mazan dake tsamanin sun auri macen da tasan mahimman abubuwan dake inganta aure sai su ga ba haka ba. Wasu mazan su kasa hakuri su karo wani auren ko kuma su hakura da zama da wacce suka auro.

Ga wasu mahimman abubuwan da duk wata mace ya kamata ta sansu, ta kuma iya wasu kamin tayi aure.

Tsafta

Dole ne duk wata 'ya mace ta koyi tsaftace jikinta da kuma muhallinta.

Wasu matan musamman wadanda suka fito daga gidajen alfarma ana samunsu da rashin iya tsaftace jiki da muhalli saboda yadda suka saba da masu musu hidima.wanda hakan ba daidai bane a tarbiya na 'ya mace.

Duk gatan 'ya mace yanada kyau ta zama mai kokarin tsaftace jikinta da kuma na muhallinta domin idan za a iya kular mata da muhalinta ba za a kula da jikinta ba. Ko muhallin nata ba ko ina bane zata bada damar a shiga ba ko a gani ba.

Ilimi

Yana kan gaba ga kowace mace ta samu kamin tayi aure.

Illimi na addini ya wajaba akan iyaye su koyar da 'yar su kamin ta shiga gidan miji. Haka shima illimi na zama yana da amfani matuka a wannan lokacin da maza basu da hakuri da jimirin rike aure.

Duk macen da batada illimi zai yi wuya ta iya mu'amala da mijinta bare sauran mutane. Haka kuma abunda zata haifa suna cikin matsala na yadda uwarsu batada illimin da zata koyar dasu bare ta basu tarbiya.

Abun Yi

Lokaci na dogaro ga miji ko iyaye ya wuce. Hakan yasa kamin mace tayi aure ta tabbatar da cewa tana da wani abunda ta iya a rayuwarta da zai samar mata kudaden shiga.

Dogaro da mata suke yi katakaf akan miji na wasu bukatun da ba wajibi bane akan mazansu yake jawo rashin fahimta tsakanin ma'aurata wani lokacin. 

Wannan yasa duk namijin da kikasan bazai barki kiyi aiki ko sana'a ba ki hakura dashi kawai domin Allah bai hana mace neman kudi ba.

Hakuri

Duk macen da bazaka koyi hakuri ba tabbas bazata iya zaman aure ba.

Zaman aure gaba dayansa akan hakuri ake yinsa kowani irin miji kika aura kuwa.

Dole ne wani abun kina gani kece da gaskiya  amma zaki hakuka ki dauki laifin domin a zauna lafiya.

Iya Mu'amala

Yana da kyau ki iya mu'amala da mutane kamin kiyi aure.

Idan kina gidan aure duk wanda yazo gidanku tarbar da zaki masa shine abunda zai sa ya sake dawowa ko ya ki dawowa.

Ki sani a gidan mijinki ba ke kadai bace zaki yi rayuwa ba. Akwai abokai da 'yan uwan miji. Akwai makota ko masu muku hidima idan masu akwai ne. Dukkanin wadannan mutane dole sai kin iya mu'amalar zama da mutane kamin zaki zauna da kowa lafiya musamman ma ace kina da abokan zama.

Girki

Duk wanda ya ce miki aikin mace a gidan mijinta babu girki yaudaranki yake yi. Idan har Matan Manzon Allah (SAW) zasu masa girki har abokansa suzo suci, kamar yadda ayar Alkurani ya bamu labari, ina ga ke.

Haka nan ta wajen girki ake kara shiga zuciyar namiji. Matar data iya sarrafa abinci da kayan sha ba daya take da wacce bata iya ba a wajen mijinta.

Duk namijin dayasan matarsa ta iya girki da wuya ki sameshi yana cin abinci a waje. Koyo da iya girki kala kala kamin kiyi aure wajibi ne muddin kina burin ganin kin zauna a gidan aure.

Kyauta

Yana cikin abunda duk wata mace zata iya kamin tayi aure.

Kada ki zama mace marowaciya, kuma mai kwaro. Idan kikayi aure da wannan halin bama masu ziyartar gidanku ba hatta mijinki da yaranki bazasu ji dadinki ba.

Ba ana nufin kiyi kyautar shiga daka kiyi kuka ba. Ki bayar da abunda kika fi karfinsa. Haka abinci kada ki zama mai ruwansa ko kwaronsa, duk wanda ya shigo gidanki ya fita a koshe muddin akwai wadatar abincin. 

Adana / Ajiya

Ko takarda kika gani a kasa namijinki samu waje ki adana masa wata rana zai neman ko zai ce a yada.

Haka nan duk wani abinci da kayan da aka bari a karkashin kulawarki ki zama kina kula dasu yadda ya dace.

Ba kuma zaki iya wannan abubuwan har sai idan kin koya tun daga gidanku. Don haka kamin kiyi aure ki iya adana sirri da duk wani abu da za a baki kula dasu.

Iya Magana

Zancen da miji ba daya yake da yadda zakiyi magana da iyayenki ko kawayenki ba.

Hira da miji ana koyonsa ne musamman saboda yadda yake da mahimmanci a wajen mace.

Akwai wasu kalmomin da duk irin yadda mijinki yake da sakin fuska da wasa bazaki furta masa su ba. Haka akwai kalmomin da duk irin dacin ran mijinki bazaki fadamasa su ba. Don haka koyo da sanin kalaman da ake furtawa masoyi neman saninsu ake yi daga lokacin da kike soyayya har zuwa rayuwar aurenki.

Jima'i

Wani abu mai matukar mahimmanci da kuma karancin samu damar koyawa 'ya mace shi kamin aure.

Iyaye musamman mata sukan kasa fitowa fili su nunawa 'ya'yansu mata abubuwan ki da wadanda ake so mace ta yisu a lokacin gudanar da Jima'i da mijinta. Duk da ana samun wasu iyayen da suke baiwa wasu tsofi da suka kwarai wajen illimantar da Yan mata Jima'i kamin aure.

Rashin karantar da 'yar ki mahman abubuwan da suka dace ta sani game da Jima'i kamin aure zai iya cutar da rayuwar aurenta musamman idan mai mata zata aura, ko wanda ya taba aure. Don haka yana da kyau iyaye mata su cire kunya da tsoro su karantar da 'ya'yansu abunda ya dace su sani game da Jima'i kamin aure.

Da fatan 'yan mata zasu amfana da wannan darasin domin samun zaman aure mai inganci.

Previous News Next News