Ban yi wani mamaki ba sakamakon ganin mutanenmu (Hausawa) na yin tambaya akan asirin kudi, ko asirin kudin ganye, ko kuma hanyar da mutum zai yi kudi a cikin ruwan sanyi.
Saboda babu wanda bai son kudi, ba kuma wanda ba ya son ya yi kudi, in ko ka ji wani ya ce shi ba ya son yin kudi kace karya ya ke yi.
Don dai kawai Allah bai bashi ba ne.
Yin kudi ba laifi ba ne, ta wasu fuskokin ma rahama ce mutum ya yi kudi, Allah ya azurta shi.
To, amma wanne irin kudi ka fi so?
Ina da yakinin daga ganin irin tambayar da kake yi kana matukar son yin kudi cikin ruwan sanyi ta hanyar surkulle-surkulle da ‘yan tsubbace-tsubbace da tsafe-tsafe.
{tocify} $title={Table of Contents}
Ban ga laifinka ba don ka so ka yi kudi ta irin wannan hanyar, sai dai zan so ka sani cewa; kudi mafi alkhairi shi ne wanda aka neme shi ta hanyar halali.
Kafin na yi nisan zango wurin yi maka bayani akan hanyoyin samun kudi, zan fara sanar da kai cewa, duk wadannan bayanan da na kwaso na rubuta maka daga yanar gizo suke, kuma ba lallai su kasance gaskiya ba.
Amma a zagaye na biyu na rubutun, inda zan bayyana maka hanyoyin samun kudi ta yanar gizo, duk abubuwan da zan zayyano gaskiya ne, babu karya a ciki.
Menene Asirin Kudi
“Shi dai asirin kudi wani irin tsubbu ne wanda wadansu gurbatattun malaman zaure da kuma bokaye matsafa ke bayarwa domin mutum ya yi kudi.”
Sannan shi wannan asirin kudin kafin mutum ya samu ya yi kudi da shi dole sai ya sauka daga kan hanya, walau ya rinka shan jinin ‘dan Adam, cin namansa, bauta wa Aljani, daina Sallah, bautawa wani gunki da zai rinka kawo masa kudi da sauransu.
Kuma mafi akasarinsa, ko da mutum ya samu kudin to Allah yana cire masa nutsuwa da kwanciyar hankali rankatakab dinsu.
Zai samu kudi, amma kuma rayuwar zai yi ta ne gatanan-gatanan, ga jin dadi ga kuma rashin jin dadi.
Menene Asirin Kudin Ganye
“Shi asirin kudin ganye shi ne asirin da mutane ke yi domin juya takarda (normal paper) ta koma kudi amma fa jabun kudi. Bayan sun bayar da kudin daga baya ya koma takarda.”
A zahirin gaskiya ‘yan damfara ne ke yin irin wannan asiri na jabun kudi / kudin ganye, bayan sun gama shi sai su rinka zagayawa wuri-wuri suna damfarar mutane.
Mutum zai yi siyayya ta kudi mai ciwo daga gareka, ya kawo tsabar kudi cash ya baka.
A lokacin da ya baka za ka ga kudaden na zahiri ne, kai ba ma kai ba, duk wanda ke wurin haka zai ga kudaden nan.
Bayan ka kaisu gida, masu siyan sun daware, sai ka ga sha’afa ka ajesu, daga baya ka bude sai ka tarar sun koma tarin takardu.
Tabbas, gurbatattun malamai da bokaye su ke bada wannan asiri na kudin ganye wanda ake yin jabun kudi da su.
Bugu-da-kari, yanzu haka an jima da samun cigaban da mutum zai iya siyar maka da waya, kwamfiyuta, agogo da sauran kaya na jabu ba tare da ka sani ba.
Sai bayan ka biya kudi, ka je gida kana dubawa za ka ga ashe kwali ya siyar maka a cikin rigar waya ko wani abu daban.
Duk irin wadannan nau’ikan asirirrikan na daga cikin misalan asirin kudin ganye sakamako a karshe dai abinda ya rikide a lokacin siya zuwa original daga baya fake zai koma.
Haka kuma, gaba daya asiri ko wanne iri ne, shirka ce kuma tsafi ne. Shi ko mai tsafi ko shirka Allah ya tsine masa albarka.
Menene Asirin Kudi na Turaren Binta Sudan
“Shi asirin kudi na turaren binta sudan, wani irin asirin kudi ne wanda ake hada shi da wadansu kayayyaki hadi da kuma rubutun Al-Qur’ani mai Tsarki ana shafawa a jiki idan za a fita daga gida.”
Babu tantama mun sani cewa shi kansa wani nau’in ne na shirka, domin babu mai bai wa mutum arziki, kudi ko wani matsayi face Allah Madaukakin Sarki.
Kamar yadda wadanda suka bada fatawar wannan asiri na turaren Binta Sudan suka wallafa, sun ce wai ko sana’a ce mutum bashi da ita, Allah zai kawo masa, kuma in kasuwa ce ta turnuke nan ma Allah zai kawo budi.
Tabbas asiri gaskiya ne kamar yadda tsafi yake gaskiyar mai shi. Za ta iya yiwuwa ka gwada shi ka ga ya yi.
Amma ni dai a shawarce, ba na shawartarka da ka gwada ko da daya daga cikin nau’ikan nan na turare domin bata ne muraran.
Menene Wuridin Kudi
“Shi wuridin kudi wani irin wuridi ne da gurbatatun malamai da bokaye ke bai wa mutane suna yi domin su yi kudi, amma mafi akasarin lokuta ba ya wuce mutum ya hadu da aljana cikin dare, ko ya rinka yi wa gunki sujjada da sauransu domin ya rinka ganin kudi suna zubo wa.”
Da dama daga cikin mutane ba su yarda da wuridin nan na kudi ba saboda shirka ce, kuma bata ne muraran.
Dalilin da yasa na ce bata ne saboda muddin za ka yi sujjada ga wanin Allah wanda ba Allah ba, to ka tabbata ka bata kai tsaye.
Abin Mamaki
Na yi matukar mamaki da na ga hashtag din “Asirin Kudi” ya samu sama da makallata miliyan 6 a dandalin kallon gajerun bidiyoyi wato Tiktok.
Ashe har yanzu gargajiyancin nan yana tare da mutanenmu, ashe har yanzu mutane suna bibiye da irin wadannan dodaddun hanyoyi marasa bullewa?
In ko haka ne, to lallai iko sai Lillahi.
Ya kamata mu yi sani cewa duniya kullum canji take kawo wa mai cike da juyin-juya-hali wanda in har ba mu bi shi mun ci gajiyarsa ba to za cigaba da barinmu a baya.
Akwai sanannun hanyoyin samun kudi har a yi arziki, kamar kasuwanci na sarari a kasuwanni da na yanar gizo, daukar bidiyoyi da yin kwamadai, kirkirar manhajojin na’ura, iya aiyukan hannu na fili da yanar gizo da sauransu.
Amma menene na uzzura wa kai da lallai sai mutum ya yi kudi alhali lokacinsa bai yi ba?
Ya kamata mutanenmu su yi karatun ta natsu domin samarwa da kansu mafita wacce take bullalliya.
Kammalawa
Na so na ja wannan rubutun nawa ya yi tsayi, sai kuma na ga in har na yi shi da tsayi to ban san irin barnar da zai kawo ba.
Hakan ya sa na takaita shi domin mu fahimci irin wadannan asiran da kuma hukuncinsu a addinance da al’adance.
Da fatan za ku cigaba da bibiyar shafin nan mai albarka, kuma duk wanda ke da tambaya ko zai yi sharhi to bismillah muna maraba da kowanne sharhi naku muddin bai dauke da cin zarafi ko cin mutunci.