Bambancin da ke tsakanin Blog, Website, Forum da Search Engine


Na yi matukar mamaki kwarai da gaske lokacin da Abubakar Sani DanBahaushe ya yi wani post a shafin sada zumunta na Facebook ya nemi a fada masa bambancin da ke tsakanin blog, website, forum da search engine amma aka kasa.

Kasawar ta bani mamaki, amma kuma ba abin mamaki ba ne in har ya kasance wasu daga cikin mutanenmu ba su san abinda ke bambanta wadannan abubuwan ba.

Shi yasa na ga ya dace na yi mana bayani mai sauki akan menene blog, website, search engine da kuma forum.

Menene Blog

“Blog shi ne shafin yanar gizo (website) wanda ake yin wallafe-wallafe akansa kullum, ko duk sati, ko duk wata.”

Babu wani website da za a kira shi da suna blog muddin masu gudanar da shi ba sa yin posting na articles, videos, ko pictures akai-akai a kansa.

Za kuma ku iya kiran kowanne blog da suna “website” amma fa ba kowanne website ne za ku kira da blog ba.

Menene Website

“Website shi ne shafin yanar gizo wanda aka kirkira domin aiwatar da wani abu muhimmi guda daya, ba kuma a sabunta shi sai shekara-shekara ko bayan watanni 6.”

Misalan websites su ne; shafukan gwamnatin tarayya na daukar aiki, shafin kidaya, shafi INEC, shafin Jamb, shafin daukar aikin Soja da sauran shafukan yanar gizo na kamfanunuwa.

Menene Forum

“Shi forum shafin yanar gizo ne wanda al’umma daga sassa dabam-daban na duniya ke ziyarta su tattauna a kan abubuwa (darussa) mabambanta.”

Misalan forums su ne; Nairaland, Quora da sauransu.

Kuma cike ya ke da dokoki da ka’idojin amfani kamar yadda shafuka dandalin sada zumunta suke. 

Menene Search Engine

“Search engine shi ne shafin da ke aje bayanan sauran shafukan yanar gizo (in har an ba shi umarnin ya aje su), ya kuma ke ciro bayanan na su domin ba da amsa madaidaiciya yayin da masu amfani da shi suka tambayeshi.”

A takaice dai shafi ne wanda ya kasance manemar bayanai wanda mawallafan shafuka ke wallafawa a shafukansu.

In har ka tambayi search engine, “yadda ake” to zai duba ne a cikin ma’ajiyarsa ya baka nuna maka bayanai da inda za ka samu amsar abinda ka tambaya ta hanyar jerin links zuwa shafuka da kuma amsar kai tsaye.

Misalan search engines su ne; Google, Bing, Yandex, Duckduckgo, Ask.com, Wikipedia da sauransu.

Kammalawa

Babu yadda za a yi ka kira Google da sunan blog, ko ka kira Nairaland da sunan blog. Kowanne a nasa mazaunin ya ke, kuma akwai amfaninsa. Da fatan za ku amfana da wannan.

Allah shi kyauta.

Previous News Next News