Maganin Sanyi Kowanne Iri

Maganin Sanyi
Maganin Sanyi

Maraba da zuwa shafin nan mai albarka.

Yau cikin ikon Allah za mu kawo muku sahihin maganin sanyi na gargajiya, wanda za ku iya hada shi da kanku cikin sauki.

{tocify} $title={Table of Contents}

Hakika ciwon sanyi ya jima yana ci wa mutane da dama tuwo a kwarya, kullum su ne sha wannan, tsotsi wancan, tauna wannan da sauransu.

Da yardar Allah sauki ya zo gareku.

Maganin Sanyi da Tafarnuwa

Hadin maganin sanyi na farko da za mu kawo muku shi ne wanda ake hada shi da tafarnuwa.

In kuma ka kasance cikin mutanen da basu son jin ko da warin tafarnuwa ne, bare shanta ko hadiyarta, to a shawarce sai ka jira wanda za mu kawo nan gaba.

Ku nemi;

  1. Danyar citta
  2. Tafarnuwa
  3. Kanumfari

Yadda ake hada shi

Da fari ku samu danyar cittarku, sai ku dakata a turmi, bayan kun dakata ta yi lilis, sai ku debeta ku aje wuri guda a mazubi.

Sai ku samu tafarnuwarku, ita ma ku saka ta a turmi ku daketa har sai ta yi lilis, sannan ku debta ku aje gefe.

Ku samu kanumfarinku, shi ma ku dakeshi ya yi lukwui, ku debeshi ku aje gefe.

Also Read: Shin Mutum na da bukatar gyara (Shan maganin karfin maza) don zai yi aure? Binciken Masana

Kai tsaye bayan kun gama daka mahadannan, sai ku debi cittarku kamar cokali biyar, da tafarkuwa cokai biyu, da kanumfari cokali biyu ku hadesu wuri guda ku gauraya.

Bayan kun gauraya, sai ku samu wuri ku adana, ku rinka dafa shafi da safe kuna diba hadin maganin nan rabin cokali kuna zubawa a ciki kuna sha sau biyu a rana (Safiya da daddare).

Insha Allahu cikin sati biyu za ku ji ku wasai, sanyin da ke masifar damunku ya nemi sa’a.

Maganin Sanyi na Mata

Ina da cikakken yakini akan hadin farko na maganin sanyi da muka bayar sadidan ne, kuma za ku ji dadinsa.

Kuma kowanne daga cikin hadin magungunan nan yana maganin sanyi na mata.

Kun san shi sanyin mata shi ake kira da sanyin mara, to da yardar mai duka in dai kuka hada wannan karyar sanyin mara ta kare.

Domin hada magani na biyu.

Ku nemi;

  1. Saiwar bini-da-zugu
  2. Saiwar kurukuru
  3. Ciyawar doddori
  4. Jar Kanwa

Yadda ake hada shi

Tabbas hada maganin sanyin nan na biyu yana da matukar sauki kwarai da gaske.

Kai tsaye da zarar kun nemi kayan hadin da na lissafto (bini-da-zugu, kurukuru da doddori), sai ku hadesu wuri guda ku zuba su a cikin tukunya, ku rinka dafasu da jar kanwa kuna diba kuna sha.

Ku yi haka har tsawo akalla sati guda, da yardar Allah Buwayi gagara misali za ku ga canji.

Maganin Sanyi Ingantacce

Za ta iya yiwuwa ka jima kana shan maganin sanyi, amma ba ka taba shan wannan ba.

Kwarai, hakan ya sa na yi tunanin lallai ya zama wajibi na yi bincike zuzzurfa domin kawo maka hadi sahihi wanda ya ke ingantacce.

Domin hada wannan maganin, sai ku nemi;

  1. Ganyen bishiyar turare (dogon yaro)
  2. Ganyen ciyawar baru‘ku
  3. Ganyen goruba
  4. Jar kanwa

Yadda ake hada shi

Ku samu shi wannan ganyen dogon yaron, da ciyawar baruqun da ganyen gorubar sai ku hadesu wuri guda ku saka a cikin tukunya ku tafa su.

Bayan sun tafasa, sai ku kawo jar kanwa ku madaidaiciya ku zuba a ciki ku kara bari ya tafaso.

Sai ku sauke shi. 

Bayan ya yi sanyi, sai ku rinka tsiyayarsa kuna sha sau biyu a rana (safiya da daddare).

Ku yi haka na tsawon makonni biyu, za ku ga sauyi da yardar Allah.

Kammalawa

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda ya bamu dama da ikon kawo muku nau’ikan maganunguna ciwon sanyi har kala uku sadidan.

Dukkanin wadannan magunguna mun samo su ne daga wuri sahihi, kuma suna aiki. Mu dai fatanmu Allah ya sa ku amfana da kowanne daga cikinsu. 

Previous News Next News