Ma'aurata |
Daga Tsangayar Malam Tonga
Da yake yanzu ne kuka soma zama, kwana da tashi a tare, a yanzu ne ko wannenku zai fahimci gaskiyar yadda rayuwar aure yake. A yanzu ne zaku gane ko soma fahimtar halayenku na gaskiya.
A shekarun farko na zaman aure da akwai wasu rashin fahimtar da ma'aurata sukan iya fuskanta a zaman auren su kamar haka:
Jima'i
A wannan lokacin ko dai shi namiji ya soma damun matarsa da yawan jima'i ita kuma bata so ko kuma ya kasa damunta da shi ita kuma tana so.
A irin haka ne za a soma samun rashin fahimtar har sai bayan an samu fahimtar juna na daidaito.
Rashin 'Yanci
Mace zata ga duk inda take son zuwa a yanzu sai ta tambaya. Ko sai an amince mata.
Shima namini idan bai dawo gida a kan lokaci ba sai amaryarsa ta nuna bacin ranta.
Wannan rashin samun damar yadda ma'auratan suke so a yanzu yakan iya zame musu rashin fahimtar da sai an sabu matsala.
Also Read: Hanyoyin da za ka sa Masoyiyarka ta shaku da kai
Haka nan da akawai wasu abubuwa da damar gaske da suke iya yinsu kamin suyi aure ba tare da neman izinin wani ba ko tunanin wani zai hana ba sai suga yanzu fa ba haka abun yake ba.
Kashe Kudi
Kamin auren namiji zai ga bai kashe wasu kudi masu yawa a kullum ko a wata. Yanzu kuma da yin aure sai yaga yawan kudin da yake kashewa suna da yawa.
Ita kuma mace kamin aure duk abunda take tana so shi ake saya mata. Yanzu anyi aure maimakon taga hakan ya dore sai taga ba haka abun yake ba. Daga nan sai rashin fahimta ya kunnu kai.
Haihuwa
Akwai matan da suna haihuwa zasu watsar da hidimar kula da miji hankalin su ya dawo kan jariri.
Haka nan akwai mazan da idan aka musu haihuwa idanuwan su na kan yadda uwar yar ke kula da shi. Duk abunda tayi ba daidai bane bare ace jariri yayi kuka laifin uwa ce. Wannan har sai ya haifar musu da matsala kamin nan gaba su goge da rayuwar zama iyaye.
Tsafta
Kamin aure basu da masaniyar hakikanin yadda suke da tsafta. Yanzu zama waje guda ya kamasu sai suka gano cewa angon ashe dai kazami ne.
Ko kuma amaryarce kazama.
Wannan matsalar zai sa su samu matsala na rashin fahimta. Cikin shekara guda idan aka yi dace guda ya gyara guda.
Kula da Addini
Akwai wasu matan sai namiji ya aurosu yake iya ganowa basu da kula da addini.
Bata damu da kula da lokacin yin sallah na farilla bama bare na nafila. Gaba daya addini bai gabanta.
Sai tarin karatu wanda abunda mijin ya gani kenan ya aura.
Akwai mazan da idan suna cikin mutane suka yi sallah tare da mutane. Amma muddin suna gidansu basu damu da kula da sallah ba. Wanda hakan zai iya zama matsala tsakaninsu da matansu idan masu kula da addini ne.
A shekara guda na zaman aure, akwai wasu abubuwan da ma'aurata zasu iya gani da fahimtarsu a zahiri game da abokan auren su. Wasu kuwa sai bayan rashin wadata ko an samu wadatar suke iya fahimtar junansu.
Koma dai menene, sirrin zaman aure sune hakuri da fahimtar juna.