Yanzu-Yanzu: Mutane 5 sun Mutu sakamakon fashewar Silindar Gas a Jihar Sokoto

Sokoto Police
Sokoto Police


Mutane 5 ne ake fargabar sun mutu wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon fashewar wasu abubuwa a garin Isa da ke karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Wani mazaunin yankin mai suna Sanusi Surajo ya shaida wa Aminiya cewa fashewar ta faru ne da tsakar ranar Lahadi.

“Ina gida sai na ji wata kara. Lokacin da na fito sai na gano cewa silinda na walda ce ta fashe.

“Mutane uku ciki har da mai shagon ne suka mutu nan take, kuma gawarwakinsu ya yi tsaga.

“Yan sanda sun yi amfani da buhu don kwashe sassansu. An ce wani mutum ya mutu daga baya a asibiti yayin da wani dan kasuwa a unguwar ya rasa hannunsa daya aka garzaya da shi asibiti domin yi masa magani,” inji shi.

Wani mazaunin garin Usman Muhammad ya ce ya kirga gawarwakin mutane biyar a wurin da fashewar ta afku.

“A yanzu haka ina wurin da fashewar ta faru. Na kirga gawarwaki biyar sun lalace sosai.

“Kuma na ga wasu daga cikin wadanda suka jikkata, ciki har da ma’aurata. Wasu daga cikinsu ko dai kafafunsu ko hannayensu sun lalace,” inji shi

Shugaban karamar hukumar, ya ce ba ya garin lokacin da lamarin ya faru don haka ba zai iya bayar da cikakken bayani ba.

"Amma muna yin tuntuɓar juna da tattara bayanai don ayyukan da suka dace," in ji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya ce ba a yi masa bayanin faruwar lamarin ba.

Previous News Next News