Daga Tsangayar Malam Tonga
A darusan mu na baya, munyi darasi ne akan yadda mata suke inzali da kuma abunda yasa suke yi. A wannan darasin zamu yi bayani ne akan alfanun da mata suke samu idan suka yi inzali.
Duk da yake ba duk mata suke samun damar yi zuwan kai ba. Sai dai kuma duk mata suna iya yin zuwan kai idan suka samu dacewa da miji.
Da akwai wasu alfanun da mata masu zuwan kai suke samu idan sunyi zuwan kai.
Da farko dai, shi zuwan kai ga mata yakan sasu kara kauna da son mazansu. Duk wata macen da take samun damar yin zuwan kai a lokacin saduwa da mijinta. Za a ga cewa tana matukar nuna masa so da kauna. Wanda duk matsain da take fuskanta a gidansa yana da wahalar gaske aji tana neman saki.
Alfanu na gaba da mata suke samu a daliin yin inzali shine na samun karin lafiya. Matar da take yin Jima'i ba tare da yin zuwan kai ba, ba daidai take da macen da take yi ba a lafiyar jiki dana kwakwaluwa.
Alfanu na uku ga mata masu yin inzali shine, na tabbatar wa mace ainihin dadin Jima'i.
Duk da yake matan da basa zuwan kai suma suna jin dadin Jima'i. Amma ita macen da take inzali itace tasan kololuwar jin dadi na Jima'i. Wannan alfanun yakan sa taji ita cikenkiyar macece.
Kamin mace ta fahimci tanada cikenken Lafiyar Jima'i, har sai ta samu damar yin zuwan kai a nan ne ma zata fahimci tana da lafiya amma fa ba ana nufin cewa macen da bata zuwan kai bata da lafiya bane. Amma a jimaince da sauranta.
Haka nan idan mace tana zuwan kai tana samun damar warware gajiyar dake jikinta. Da kuma gushewar damuwa a ranta.
Macen da bata zuwan kai koda tayi Jima'i bata samun yin wani annashuwa da walwala kamar yadda mace mai zuwan kai take yi.
Da zaran mace tayi zuwan kai tana samun yin bacci mai dadi ga kuma gushewar gajiya daga jikinta.
Kaman yadda muka yi bayani a baya. Ba duk mata bane suke yin zuwan kai ba. Amma kuma duk wata mace zata iya yin zuwan kai muddin ta samu namijin dazai iya ganota. Da fatan mata zasu taimakawa mazansu gano hanyoyin da zasu iya bi domin gamsar dasu.