Kunun Aya |
Yau, za mu koyar da yadda ake yin kunun aya, bayanin da za mu yi dalla-dalla ne mai saukin fahimta.
Daidaiku ne cikin mutane wadanda ba sa son kunun aya, kuma ba sa son shan sa.
Amma in za ka yi lissafi, kada ka lissafo da ni, domin ni babban masoyinsa ne.
Kayan Hadin Kunun Aya
Domin hada kunun aya mai dan karen dadi sai ka nemi;
- Aya
- Sikari
- Kwakwa
- Dabino
- Flavour
- Madara
Ku sani cewa, su wadannan kayan hadin akwai daga cikinsu wadanda ba su zama wajibi ba, sai in akwai halin siyansu a saka a ciki.
Yadda Ake Yin Kunun Aya
<> Da farko dai, ki samu ayarki sai ki bece ta, ki wanke ta, ki rairaye duk tsakuwar da ke cikinta, sai ki zuba ta a ciki.
Sai ki zuba mata ruwa ki barta ta yini ko ta yi wadansu 'yan awanni.
<> Abu na gaba, sai ki kawo dabinonki ki gyarashi, ki cire kwallonsa, ki yayyankashi kanana ko ki tsatstsagashi.
Also Read: Yadda Ake Kunun Gyada (bayani dalla-dalla)
<> Abu na gaba, sai ki kawo kwakwarki ki yayyanka ta kananu yadda za ta nuku.
<> Abu na gaba, sai ki tsame ayarki daga ruwa, ki zuba a mazubi, ki kawo dabinonki ki zuba, ki kawo kwakwarki ku zuba, sannan ki saka a bleding machine ki yi blending, ko kuma ki kai inji a markada miki don zai fi yin laushi.
A injin, ki gargadi mai nikan a kan kada ya saka miki ayarki akan wake ko kayan miha, ki wani abu makamancinsa, kuma ya dauraye kan injinsa.
<> Abu na gaba, bayan kin niko, sai ki saka mataci na tatar koki ki tace markaddiyar ayarki (ki ware duba daban, kulli daban).
Kullin shi ne wanda za ki kawo sikari da flavour ki zuba masa, in ma kina da halin saka madara ta gari ta ruwa ko ta gari ki kasa.
In akwai wata 'yar kankara ki kawo ki saka, sai ki gauraya, ki barshi ya yi sanyi yadda zai yi dadin sha.
Saboda kunun aya in babu sanyi bai cika dadi ba.
<> Abu na karshe, za ki iya zubawa a cikin kofi a sha, ko ki dura a cikin robobi ki sayar.
Amma ki yi sani cewa, shi fa kunun aya ba kamar zobo ba ne, wanda zai yini cikin roba bai lalace ba, shi ba ya jimawa ya ke lalacewa shi yasa ake gaggawar siyar da shi ko amfani da shi.
In kina so kada ya lalace da wuri, sai ki barshi ciki freezer ko kuma cikin kankara.
Kammalawa
Ba kowacce mace ce ke hada kunun aya kamar yadda na yi bayani ba, wasu suna malkado ayarsu suka tace, sai su zuba sikari shikenan sun gama sai kankara.
Ki hada irin naki kunun ayar daidai karfinki, babu dole a rayuwa, abinda zai yiwu shi ake yi.
A cikin wannan takaitaccen rubutun mun koyar da yadda ake hada kunun aya cikin sauki.