Yadda Ake Kunun Gyada (bayani dalla-dalla)

Kunun Gyada
Kunun Gyada


Yau, zan koyar da yadda ake yin kunun gyada mai dadi, cikin sauki ba tare da an sha wahala ba.

Mutane da dama na da matukar son shan kunun gyada, wasu ma har siyanshi suke yi in ana tallansa.

Baya ga dadin da Allah ya hore wa kunun gyada, akwai karin kuzari da ya ke sanya wa kamar yadda cabohydrate ya ke yi.

Har-ila-yau, gyada na dauke da sinadarin niacin wadda shi ke bada gudunmawa wurin karkasa cabohydrate zuwa energy a jikin 'dan Adam.

In har muka yi duba da wadannan tarin fa'idoji na mu'amala da kunun gyada, to lallai ba za mu daga masa kafa ba.

Kayan Hada Kunun Gyada

In har da gaske ki ke son yin kunun gyada, sai ki tanadi;

  1. Shinkafa (daidai bukatarki)
  2. Gyada (ki soyata sannan ki bakace ta)
  3. Sai lemon tsami
  4. Sai kuma citta in kina so

Yadda Ake Yin Kunun Gyada

Da farko dai, ku samu tukunya mai dan zurfi, sai ku zuba gyadarku a ciki, ku soya ta sama-sama, sannan ku sauke ku bakace ta (bi ma'ana murje ta).

Abu na gaba, sai a samu bokiti ko robar nika, a zuba shinkafa da gyadar nan da kuma citta a ciki a kai markade.

Bayan an niko, sai a saka mataci a tace wannan markaden a ware kulli daban, dusa daban.

Abu na gaba, sai a samu wankakkiyar tukunya wacce za ta cinye gasar nan, sai a zuba kullin a ciki, a kawo ludayi a rinka juya gasarar kamar damun koko har sai an tabbatar ta yi kauri.

Abu na karshe, da fatan an yanka lemon tsami an matse ruwan, sai a kawo ruwan lemon tsamin nan a zuba a ciki, a 'dan debo, a 'dan'dana a ji ko ya yi daidai.

In ya yi daidai, to kunun gyada ya yi yadda ake so.

A kula: kada a zuba lemon tsamin ya yi yawa, kuma kada ya yi kadan, a zuba daidai misali.

Kammalawa

A cikin darasin nan namu na yau na koyon hada kayan shaye-shaye, mun koyar da yadda ake kunun gyada cikin sauki.

Duk bayanan da muka yi, mun yi su ne dalla-dalla.

Previous News Next News