Zulum ya hana sana'ar bola-bola da gwangwan a fadin jihar Borno

Gwamna Zulum


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanya dokar hana yin sana'ar gwangwan da bola-bola a fadin kananan hukumomi 27 na jihar har abada.

Zulum ya ce ya hana sana'ar ta gwangwan da bola-bola ne domin dakile cigaba da kashe masu sana'ar da 'yan ta'addan Boko Haram ke yi a wasu sassan kananan hukumomin jihar, da kuma dakatar da satar kayan gwamnati da na al'umma da wasu daga cikin masu sana'ar ke yi.

Gwamna Zulum da yake sanar da dokar haramta sana'ar a ranar Litinin a Maiduguri, ya ce, “A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kashe mutane da dama a sakamakon bola-bola (neman karafa).  Hakan ne ya ankarar da gwamnatin jihar Borno da ta binciki irin wadannan munanan ayyuka,” 

Ya kara da cewa, “Kun ga wannan wurin, duk wadannan kadarori ne na gwamnati kuma a bayanku akwai kadarori na kamfanonin sadarwa.  Irin waɗannan ayyukan dole za a sanya su matsayin zagon ƙasa ga gwamnatocin tarayya da na jihohi.  Don haka na ba da umarnin hana fasa-kwaurin karafa (gwangwan) a dukkan kananan hukumomi 27 har sai inna ta gani.”

Also Read: Zababben ‘Dan Majalisa Jiha, Dr Nuhu Clerk Ya Rasu a Borno

Zulum ya yi bayanin cewa, wadannan ‘yan gwangwan din sun yi kaurin suna wajen lalata dukiyoyin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a galibin kananan hukumomin da ta'addancin 'yan Boko Haram suka tilasta wa mazauna yankin yin hijira.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi asarar kadarori masu kima na biliyoyin Naira a cikin shekaru biyar da suka gabata sakamakon ayyukan ‘yan gwangwan din.

Gwamnan ya ce dokar hana fasa kwaurin karafan (gwangwan) ta shafi duk wani nau’in gyaran karafa da ba a kayyade ba, wanda ya hada da wargajewa, tarawa da safarar karafa.

Ya yi gargadin cewa gwamnatin Borno za ta hada gwiwa da jami’an tsaro don aiwatar da dokar yadda ya kamata ta hanyar zartar da hukunci mai tsauri kan masu karya dokar hana gwangwan din.

Previous News Next News